A ran 2 ga wata da sassafe,sai da bangarorin biyu suka yi musayar wuta a Zlitan birni mafi muhimmanci dake yammacin Tripoli babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 na kungiyar adawa yayin da wasu 50 suka raunana.
A sa'i daya kuma,an kasa samun zaman lafiya a sararin tekun Libya. A ran 3 ga wata, jirgin yaki mai dauke da makamai masu linzami da ake kira "Bersagliere" na kasar Italiya wanda ke shiga matakin sojan da NATO ta dauka da zummar kai hare-hare kan Libya, ya gamu da harin da aka kai shi.
Wani Manazarci ya lura da cewa, rikicin Libya ba zai kare a cikin gajeren lokaci ba. Game da halin da ake ciki kuwa a yanzu, ya ce, kasashen yamma na goyon bayan kungiyar adawa da zummar dakile mulkin Gaddafi, hakan ya sa kungiyar ta tanadi isasshen kudi, makamai da kayayyakin yau da kullum ta yadda za su yi gwagwarmayya cikin dogon lokaci.(Amina)