Ministan harkokin sadarwa na gwamnatin kasar Habasha Berek Simon, ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa, za a yi jana'izar marigayi firaministan kasar Habasha Meles Zenawi a ranar 2 ga watan Satumba.
Lokacin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a otel din Hilton International da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, Berek ya ce, za a gudanar da jana'izar marigayi firaministan a ranar 2 ga watan Satumba a Addis Ababa.
Berek ya ce, an kafa kwamitin kasa da kuma kananan kwamitoci don ganin an gudanar da jana'izar yadda ya kamata.
Ya kuma shaidawa manema labaran cewa, tuni wasu shugabannin kasashe suka tabbatar cewa, za su halarci jana'izar yayin da ake sa ran, wasu ma za su tabbatar da zuwan nasu.
Ministan ya kuma bayyana cewa, al'ummar kasar Habasha sun bayyana kudurinsu na ci gaba da bin ayyukan da marigayin ya fara tare da ci gaba da aiwatar da manufofi da dabarun da Meles da gwammatinsa suka kirkiro.
Berek ya ce, mataimakin firaministan kasar Hailemariam Desalegn, shi ne zai ci gaba da rike mukamin firaministan kasar, har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a shekara ta 2015.
Ya ce, kundin tsarin mulkin kasar Habasha ya bayyana cewa, mataimakin firaminista ne zai maye gurbin firaministan, idan babu firaminista.(Ibrahim)