in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Sin da Mexico
2013-06-05 16:56:44 cri

A ranar 4 ga wata, a birnin Mexico, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Mexico Enrique Peña Nieto sun yi shawarwari, inda suka amince inganta hadin gwiwar sada zumunta cikin dogon lokaci a tsakanin kasashen 2, don ya dace da babbar moriyar kasashen biyu da jama'arsu, abin da hakan zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

Shugabannin kasashen biyu sun sanar da cewa, za a inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Sin da Mexico daga dukkan fannoni.

Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen 2 sun rattaba hannu a kan 'Hadaddiyar sanarwa tsakanin Jamhuriyar Jama'ar Sin da Hadaddiyar kasar Mesico', kuma sun gani da idanunsu yadda aka daddale yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa a fannoni da dama, kuma sun gana da manema labaru tare.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China