in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Costa Rica sun tattauna yarjejeniyar hadin gwiwwa
2013-06-04 10:15:11 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da yanzu haka yake ziyara a kasashen waje ya gana da takwararsa ta kasar Costa Rica Laura Chinchilla a jiya Litinin inda suka tattauna yarjejeniyar cigaba a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na kasar Sin, kafin haka sai da ya halarci bikin maraba da shugaba Laura ta shirya masa kafin fara wannan tattaunawa, ana sa ran tare da mai masaukin bakinsa za su shaida rattaba hannu a kan yarjejeniyar ta hadin gwiwwa da wakilan kasashen nasu za su yi sakamakon tattaunawarsu.

Shugaba Xi da yanzu haka yake a cikin zangonsa na biyu na ziyararsa a kasashen waje da fari dai sai da ya isa kasar Trinidad da Tabago, kuma daga kasar Costa Rica zai isa Mexico daga nan kuma ya yada zango na karshe a kasar Amurka.

Wannan ne dai ziyarar shugaba Xi na farko zuwa yankin Latin Amurka tun darewarsa karagar mulki a watan Maris.

Makasudin wannan ziyarar ta shugaba Xi a kasashen Latin Amurka kamar yadda ya sanar a wata sanarwa ta hadin gwiwwa da shugabannin kasashen da ya ziyarta lokacin ganawarsu da manema labarai shi ne domin a karfafa dankon zumunci tsakanin kasar Sin da yankin Latin Amurka tare da fadada huldarsu ta amintaka da za ta amfani dukkan wadannan kasashe.

Shugaba Xi ya ce, yana da cikakken imanin cewa, wannan ziyarar zata kara karfafa wani nau'in aminci da hadin gwiwwa da yanzu haka kasar ke yi tare da wadannan kasashe domin samar da daidaito, amince ma juna, da kuma cigaba tare.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China