Ministan masana'antu, cinikayya da zuba jari na kasar Najeriya Dr. Samuel Ortom ya ce, Najeriya ce ke kan matsayi na 26 a fadin duniya a fuskar samar da manja, kuma wanda take samarwan ba ya isan bukatu na cikin kasar.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta masu ruwa da tsaki da aka yi yau, a hedkwatar ma'aikatar a garin Abuja, dangane da cimma nasarar shirin babban taron kasa da kasa kan manja, (IPPC), jiko na farko.
A cikin jawabinsa da babban sakataren ma'aikatar Mr. Dauda Kigbu ya karanta a madadinsa, Dr. Ortom ya ce, irin yadda aka gagara cimma bukatar cikin gida na manja ya nuna irin babbar koma baya da aka samu.
Ya ci gaba da cewa, saboda wannan dalili, kungiyar masu samar da manja ta kasa (NPPAN) tare da hadin gwiwar ma'aikatar za su shirya wani taro da nufin yin tattaunawa da kuma musayar ra'ayoyi da masu ruwa da tsaki a wannan harka a fadin duniya, kan yadda za'a bullo da sabbin dabarun tinkarar wannan batu da nufin farfado da masana'antar samar da manja a kasar Najeriya.
Ortom ya ce, za'a shirya wannan taro ne a daidai lokacin da ma'aikatar ke dasa tubalin kawo canji a masana'antar manja, a matsayin wata hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki.
Ya ce, shirin ya dace domin zai janyo hankalin masu zuba jari da masu ruwa da tsaki a wannan masana'anta a Afirka, da ma wasu kasashen duniya sama da 40.
Ya ba da tabbacin cewa, ma'aikatar za ta ci gaba da bullo da manufofi da suka dace da za su kai ga habbakar masana'antun kayyayakin masarufi, a dukkan matakai domin a samu farfado da masana'antar samar da manja. (Lami)