A ranar Alhamis, shugaba Goodluck Jonathan na kasar Najeriya ya kaddamar da wata sabuwar manufar wasanni a matakin karkara mai taken 'Rhythm and Play' a Turance.
Shugaban na Najeirya ya ce, ana kan shirin mayar da shiga harkar wasanni ta zamo wajibi ga dukkan daliban makarantun firamare da sakandare a kasar.
Ya kara da cewa, tsara manufar hakan shi ne domin a horar da 'yan wasa da za su wakilci kasar a gasar wasanni na kasa da kasa.
Ya ce, an cimma wannan shawara ne bayan wani zaman shawarwari da aka yi a watan Oktoban bara a kan wasanni, wacce kuma ke da nufin gina kasar da ta dacewa matasa.
Shugaba Jonathan ya ce, wannan manufa za ta kawo babban canji a fuskar harkokin wasanni a yankunan karkarar Najeriya.
Ya ce, kasar ta yi abin a zo a gani a fuskar wasanni a baya bayan nan, don haka ake bukatar samar da manufofi da za su tabbatar da ci gaban nasarar da aka samu. (Lami)