Likitocin kasar Faransa, da aka baiwa nauyin kula da lafiyar shugaban kasar Mauritania da ya sami rauni bayan an harbe shi da bindiga wanda kuma yake samun jinya a yanzu haka a birnin Paris, sun gargadi shugaban kasar na Mauritania a ranar Lahadi da ya tsaya domin cigaba da samun jinya a hedkwatar kasar Faransa, a cewar wata majiyar diplomasiyya.
"Lafiyar shugaban kasar na cigaba da samun kyautatuwa kuma a ranar Lahadin da ta gabata, ya samu yin hira ta wayar tarho tare da manyan jami'an kasarsa da suka bukaci sanin halin da yake ciki da kuma lafiyar jikinsa." in ji wannan majiya tare da jaddada cewa, shugaban kasar Mauritania zai iyar komawa kasarsa a tsawon makon farko na watan Nuwamba mai zuwa. (Maman Ada)