in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an tsaron kasar Guinee-Conakry sun bayyana wata dabarar yaki da fataucin kananan yara
2012-11-06 15:38:28 cri

Babban kwamandan jandarman kasar Guinee-Conakry ya gabatar a ranar Litinin da wata dabarar daukar kwararrun matakai na ladabtarwa domin yaki da fataucin kananan yara, a yayin bikin mika wasu yara biyu ga iyayensu da aka sace a makon da ya gabata.

Domin yaki da fataucin yara dake kamari a kasar Guinee, babban komandan jandarma ya yi ikirarin daukar matakan bincike da hukunta mutanen dake da hannu kan fatauci da kasuwancin 'dan adam a cikin kasar.

Baya ga matakan bincike na jami'an tsaro a cikin gida, za'a kuma kafa tashoshin bincike a kan iyakokin kasashen dake makwabtaka da kasar Guinee, domin sanya hannu kan kungiyoyin dake wannan muguwar sana'a ta fataucin kananan yara a wannan shiyya ta yammacin Afrika.

Haka kuma za'a kafa rukunonin jami'an tsaro na hadin gwiwa tsakanin 'yan sanda, kwastan, da jandarma domin sa ido wajen ratsa iyaka, tare da shiga ko fitar kananan yara a lokacin da suke tare da manyan mutane.

A cewar jami'in dake kula da watsa labarai na babban kwamandan jandarman kasar, mista Mamdou Alpha Barry, an samu wasu miyagun mutane da suka sace kananan yara biyu a makon da ya gabata, inda wata mace ta sace yaro na farko daga hannun iyayensa ta hanyar cewa ita dangi ce, da wani mutum da ya sace wata karamar yarinya mai shekaru uku da haihuwa. Amma daga karshe an kwato wadannan yara da aka sace daga hannun wadannan mutane, in ji mista Barry. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China