Kamar yadda tsarin tafiyar tasa ta nuna a takarda da aka baiwa kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, shugaban zai jagoranci tawagar kusoshin masu gudanar da tattalin arzikin kasar Najeriya zuwa taron duniya kan tattalin arzikin Afirka wanda za'a bude a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu.
Ana sa rai cewa shugabannin shiyoyi da na duniya za su hallara a dandalin domin tattaunawa kan sabbin dabarun bunkasuwa da kuma fadada tattalin arziki gami da samar da muhimman ababan more rayuwa a nahiyar.
Mahalarta taron za su sabunta sadaukar da kai ga samar da wata alkibla ta bunkasa wacce za ta kai ga kara nuna dimbin albarkatu da fasahohin Afirka. Shugaban Najeriya da tawagarsa kuma za su halarci dandalin bunkasa Afirka wanda za'a yi hadin gwiwar gudanarwa a Cape Town tsakanin kungiyar hada kan kasashen Afirka, sabuwar manufar hadin gwiwa da bunkasa Afirka da kuma dandalin tattalin arziki na duniya. (Lami Ali)