in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren adawa a Guinea zai janye wakilai daga hukumomin jam'iyyar Republic
2012-06-14 13:51:36 cri

Yan adawa a kasar Guinea da suka hada da jam'iyyar siyasa wato kungiyar shimfida demokuradiya ta ADP, a halin yanzu, suna kokarin janye wakilansu daga cikin wasu hukumomi na jam'iyyar Republic. Daga cikin hukumomin da 'yan adawar ke janye wakilansu, akwai kwamitin zabe mai zaman kansa wato CENI da kwamitin rikon kwarya na kasar wato CNT, da cewar Sidya Toure, daya daga cikin shugabannin 'yan adawa. An dauki wannan mataki ne sabili da rage muhimmancin hukumomin wato CENI da CNT a idon jama'ar kasar Guinea da na jama'ar kasa da kasa baki daya.

Sidya Toure na bangaren adawa ya furta cewa, daga nasu bangare, kwamitin rikon kwarya na kasar bai gudanar da aikinsa wajen kiyaye moriyar jama'ar kasar Guinea yadda ya kamata ba. Ya jaddada cewa, ya kamata kwamitin ya dauki hakki bisa wuyansu a fannonin kafa dokoki da shirya zabe kamar yadda sauran kasashe kamar su Nijer da Cote Divor suka yi.

Idan aka kafa majalisar dokoki a kasar, to, za a kammala wa'adin aikin kwamitin rikon kwarya da ya dade yake aiki a kasar. Hakan zai bude wani sabon shafi a kasar Guinea tare da samun jari daga kasashen waje. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China