in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron kasa da kasa kan matsalar tsaro a yankin Sahel
2012-12-12 10:13:12 cri

Matsalar tsaro dake kamari a yankin Sahel da kuma munanan kalubalolin da take haddasawa kasar Nijar sun kasance muhimman batutuwa da aka tattauna kan su a yayin wani taron kasa da kasa da ya gudana daga ranar Litinin zuwa ranar Talata a birnin Yamai, a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Nijar Bazoum Mohamed. Taron ya samu halartar kwararrun ma'aikatar harkokin wajen kasar, ofishin ministocin dake kula da batutuwan tsaro da zaman lafiya, majalisar dokoki, malam jami'a da kuma masana na kasar Nijar da na kasashen waje.

A tsawon kwanaki biyu, mahalarta taron sun mai da hankali kan halin da ake ciki a wannan shiyya, kalubale da barazana a yankin Sahel, musammun ma a kasar Nijar, haka kuma da tattaunawa tsakanin gamayyar kasa da kasa, malaman jami'a da masu fada a ji kan sabon tsarin nazari da sa ido na CEPA.

A lokacin da yake jawabi kan kaddamar da ayyukan CEPA, Bazoum Mohamed ya mai da hankali sosai kan 'yan tawaye dake kawo barazana kan tsaron kasar Nijar da suka hada da kungiyoyin masu makamai, a wasu yankuna dake kusa da birnin Yamai, babban birnin kasar, a nan minista Bazoum Mohamed na nuni da matsalar dake faruwa a arewacin kasar Mali, tashe-tashen hankali na ta'addanci na kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya da kuma tabarbarwar tsaro kan iyakoki dake janyo fataucin miyagun kwayoyi da makamai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China