Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Mr. Wang Ting da ke kan keken guragu ya kafa kamfanin kire kire injunan lantarki na birnin Xi'an na kasar Sin, shi ma ya zama daya daga cikin jama'ar da suka mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. A shekaru da dama da suka wuce, Mr. Wang Ting ya tsaya tsayin daka kan taimakawa nakasassu, bi da bi ne, ya kafa masana'antu guda 9. Hakan ya daidaita maganar samun aikin yi ga nakasassu fiye da 200. Mr. Wang Ting ya ce, burinsa shi ne, domin gudanar da wasu hakikanan abubuwa ga nakasassu. Ya ce, Lawal:"Nakasassu su kan fuskanci matsaloli a yayin da suke ganin likita, da shiga cikin makaranta, da samun ayyukan yi da dai sauransu. Dalilin da ya sa na kafa wadannan masana'antu shi ne, domin daidaita wasu hakikanan matsaloli ga nakasassu, domin nakasassu su daidaita matsaloli bisa ga karfinsu da kansu."

Lubabatu:Jama'a masu sauraro, barkanku da ci gaba da sauraron rahoton musamman na bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing daga Gidan Rediyon Kasar Sin.

Bayan bikin budewa da za a shirya a yau da dare, za a fara gasanni a hukunce na wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing. Shugaban hukumar wasannin Olympics ta nakasassu ta duniya Mr. Philip Craven ya gayyaci jama'a da su kalli gasannin Olympics. Ya ce, Lawal:"Na taba zama wani 'dan wasa na kwallon kwando da nakasassu ke yi a kan keken guragu, wanda ya fi wuya a duk duniya. Abin da nike son gaya wa masu sauraron Gidan Rediyon Kasar Sin shi ne, idan ka kalli gasannin Olympics na nakasassu da idonka, tabbas ne za ka ji mamaki sosai, sabo da haka ne, ya kamata ka shirya sosai."

1 2 3 4 5 6 7 8 9