Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Lubabatu:A waje daya kuma, a cikin nasa jawabin, Mr. Philip Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasa da kasa ya yaba wa aikin kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na Beijing sosai. Yana fatan 'yan wasa nakasassu su more wannan gagarumin biki kamar yadda ya kamata.

Lawal:"Wannan kasaitacciyar gasar Olympic ta nakasassu ce. Ko yawan 'yan wasa da yawan kasashe da yankuna da suke halartar gasar da yawan shirye-shiryen wasannin motsa jiki da za a yi a gun wannan gasa dukkansu sun wuce na gasannin Olympic na nakasassu na da. Wannan wani muhimmin lokaci ne a kan tarihin gasannin wasannin Olympic ta nakasassu. Sabo da haka, muna alfahari kwarai da gaske. Zukatanmu suna kasancewa tare da miliyoyin jama'ar Sin da suka samu jerin bala'u daga indallahi a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki. Bala'u daga indallahi ba su hana kasar Sin da ta ci gaba ba, kuma ba su iya hana kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing da shugaba Liu Qi na wannan kwamiti da su ci gaba da shirya gasannin Olympic. Gasar wasannin Olympic ta Beijing tana da kayatarwa sosai, muna da imani cewa, tabbas ne za a samu nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Ko shakka babu, a yau da dare da kuma cikin kwanaki fiye da 10 masu zuwa, 'yan wasa su hakikanan jarumai ne. Kuma za ku gane cewa, ku da mu dukkanmu muna zama a cikin duniya daya baki daya."

Lubabatu:Jama'a masu sauraro, wakar da kuke saurara ita ce "Tashi tare da mafarki", wato babbar waka ta wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu. A cikin wannan waka, ana rera cewa "Tashi tare da mafarki, Flying with the dream, mu tashi zuwa gidan gaskiya tare da mafarki." Wannan ne fatan alherin da jama'ar duk kasar Sin suke taya wa abokai nakasassu na duk duniya.

Lawal:Bugu da kari kuma, a gun bikin kaddamar da gasar, 'yan wasa nakasassu sun kuma bayyana fatansu na yin gasa cikin adalci da cika alkawarin da suka dauka da kansu. A madadin dukkan 'yan wasa nakasassu ne, 'yar wasa na kasar Sin Wu Chunmiao ta yi rantsuwa cewa, "A madadin dukkan 'yan wasan da ke halartar gasar na yi rantsuwa a nan cewa, za mu tabbatar da daukaka wasannin motsa jiki da kuma girmama kungiyoyin wasannin, za mu shiga wasannin motsa jiki daban daban na Olympic na nakasassu a fili bisa hasashen motsa jiki, kuma za mu bi ka'idojin wasannin motsa jiki da aka tsara. Kuma za mu yi kokarin shirya wata gasar da babu magungunan sa kuzari da sauran magunguna."

Lawal:A karkashin idanun dubban jama'a, an kunna babbar yola ta wutar gasar wasannin Olympic ta nakasassu. An dauki wannan wuta ce a ran 28 ga watan Agusta a Heaven Temple na Beijing. Sannan, an mika wutar ta hanyoyi biyu, wato wata hanyar nune-nunen abubuwan zamanin yanzu da wata hanyar nune-nunen al'adun gargajiya ta al'ummomin Sinawa da ke hada da birane 11 domin bayyana hasashe uku na "yin fiecewa da haduwa da morewa".

Lawal:Masu sauraro, yanzu sai a ci gaba da saurari shirin musamman game da bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing daga nan sashen Hausa na Rediyon kasar Sin.

Lubabatu:Ko shakka babu, bikin bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ya jawo hankulanmu duka, ban da wannan kuma, a gun gasar, za a kago abubuwan ban mamaki da yawa wadanda za su zama 'na farko' a tarihin wasannin Olympic na nakasassu.

Lawal:A gun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, 'yan wasa nakasassu sama da 4000 za su shiga gasannin da za a shirya, malaman wasa da jami'ai sama da 2500 za su shiga ayyukan da abin ya shafa, duk wadannan 'yan wasa da malaman wasa da jami'ai sun zo ne daga kasashe da shiyyoyi fiye da 140, adadin nan ya fi yawa a tarihi.

Lubabatu:Yanzu, a duk fadin duniya, gaba daya yawan nakasassu ya kai sama da miliyan 600, a kasar Sin kuwa, ya kai fiye da miliyan 83. Domin samar da hidima mai inganci ga nakasassu, za a yi amfani da harshen alamar hannu yayin da ake watsa labarai kan gasanni. Nakasassu za su iya samun labarai daga tashar internet ta kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta hanyar kallon alamar hotunan hannun da aka zane ta inji mai kwakwalwa. Irin wannan hidima ita ma ba a taba ganin irinta ba a tarihin wasannin Olympic.

Lawal:Ran 30 ga watan Agusta na bana, aka kafa bangon tunawa da 'yarjejeniyar hakkin nakasassu' a kauyen wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, wannan shi ne karo na farko da aka kafa bangon tunawa wanda aka mayar da yarjejeniyar majalisar dinkin duniya a matsayin babban batunsa a tarihin wasannin Olympic na nakasassu, dalilin da ya sa aka kafa bangon shi ne domin neman jama'ar kasashen duniya su bi 'yarjejeniyar hakkin nakasassu' ta majalisar dinkin duniya. Wannan yarjejeniya ta zama takardar doka ta kasa da kasa ta farko wajen kare hakkin nakasassu daga duk fannoni a tarihin majalisar dinkin duniya.

1 2 3 4 5 6 7 8 9