Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Lubabatu:Tun daga shekarar 1960 wato bayan da aka shirya zama ta farko ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu har zuwa yanzu, gasar tana da tarihi na tsawon shekaru 48. Game da asalin gasar wasannin Olympic ta nakasassu, ana iya cewa, batun nan ya bata mana rai. Mataimakin direktan sashen kula da gasar wasannin Olympic ta nakasassu na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing Wang Bingyang ya yi mana bayani cewa: Lawal:"Yakin duniya na biyu ya sa iyalai da yawa suka rasa dangoginsu, kuma a sanadiyar yakin, mutane da yawa sun zama nakasassu. A shekarar 1948, wani likitan kasar Jamus Ludwig Guttmann da wasu mutane masu aikin sa kai kan sha'anin nakasassu sun gayyaci wasu sojoji masu shanyewar kafafuwa domin shirya wata gasar kwallon kwando ta kujera mai taya, ana kiran gasar da suna 'gasar Stoke Mandeville'. Ya zuwa shekarar 1960, bayan makonni biyu da aka kawo karshen zama ta 17 ta gasar wasannin Olympic ta Rome, 'yan wasa nakasassu 400 da suka zo daga kasashe 23 sun shiga zama ta 9 ta gasar Stoke Mandeville ta duniya a birnin Rome. Daga baya kuma kwamitin wasannin Olympic na duniya ya amince da cewa gasar Rome ta zama gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta farko. "

Lubabatu:Tun daga shekarar 1960, ana shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu sau daya a shekaru hudu hudu. Tun bayan zama ta 8 ta gasar da aka yi a shekara ta 1988 a birnin Seoul na kasar Korea ta kudu, aka fara shirya gasar wasannin Olympic da gasar wasannin Olympic ta nakasassu tare kuma a birni daya. A shekarar 1989, a hukunce ne aka kafa kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya.

Lawal:A ran 28 ga watan Agusta na bana, aka rera wakar kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya a lambun shan iska da ake kira 'the temple of heaven', mai karbar wutar gasar wasannin Olympic ta nakasassu Jiang Xintian wadda ita ce 'yar fasaha bebiya daga kungiyar fasaha ta nakasassu ta kasar Sin ta kunna wutar gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Wutar ta kona sosai. An ci nasarar karbar wutar! Daga baya, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya sanar da cewa: "Yanzu mun fara mika wutar gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 ta Beijing!"

Lubabatu:Daga ran 28 ga watan Agusta zuwa ran 6 ga watan Satumba, an mika wutar a birane 11 ta hanyoyi biyu wato 'kasar Sin ta zamani' da 'kasar Sin ta wayin kai', an kuma nuna wa duk duniya manyan hasashe uku wato "nuna ficewa da haduwa da kuma morewa".

Lawal:To, masu sauraro, yanzu a cigaba da sauraren shirinmu na musamman da gidan redyion kasar Sin ke gabatar muku game da bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing.

Lubabatu:"nuna ficewa" ta kasance daya daga cikin manyan ire-iren hasashe uku na wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, kuma jigonsa shi ne wuce karfin da bil-adam suke da shi, da kuma tinkarar kalubalen wuce iyaka, ya bayyana makasudin wasannin Olympics na "Kara kai matsayi mai tsawo, da kara sauri, da kara samun karfi", wato "Higher, Swifter, Stronger" a Turanci, da kuma alkiblar wasannin motsa jiki na nakasassu.

Lubabatu:Ma'anar "Wucewa" ita ce, da farko ta bayyana karfin zuciya da imani na 'yan wasa nakasassu, wadanda su kan kawar da rashin jin dadi a jikunansu, da kuma siffanta kyakkyawan tunaninsu na cin gashin kai ba tare da kasala ba, da kuma yin fice wajen shiga wasanni.

1 2 3 4 5 6 7 8 9