Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Lubabatu: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barka da wannan lokaci. Shirin da kuke saurara shi ne shirin musamman da gidan rediyon kasar Sin ya tsara muku domin bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, kuma ni ce Lubabatu tare kuma da abokin aikina Lawal muke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Lawal: Wakar da kuke saurara ita ce Wakar Kwamitin Wasannin Olympic na Nakasassu na kasa da kasa. A ran 6 ga wata, wato yau da dare, bisa agogon Beijing, an yi bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekara ta 2008 ta Beijing a filin wasannin motsa jiki na kasar Sin, wato "Shekar Tsuntsu". Wannan ya almantar kaddamar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta shekara ta 2008 da za a shafi kwanaki 11 ana gudanarwa a birnin Beijing.

"Yanzu, na sanar da bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekara ta 2008 ta Beijing!" Lubabatu:An soma bikin kaddamar da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ne yau da dare da karfe 8, bisa agogon Beijing, kuma an yi sa'o'i 2 da mintoci 50 ana wannan biki. A gun wannan biki, da farko dai, 'yan wasa nakasassu fiye da dubu 4 da suka zo daga kasashe da yankuna 147 sun shiga filin motsa jiki, sannan an yi nune-nunen wakoki da raye-raye da wasannin kwaikwayo. An rarraba wannan biki kashi 3, inda aka bayyana tunanin "dukkan rayuka suna da daraja da mutunci da kuma mafarki daya" bisa babban take na "duniya daya, mafarki daya" da na "yin fice da haduwa da morewa". Shugabanni da manyan baki da suka zo daga kasashe fiye da 10 da 'yan kallo fiye da dubu 90 da ke cikin filin motsa jiki na "Shekar Tsuntsu" sun kalli wannan biki mai jawo hankulan mutane sosai tare.

A lokacin da yake jawabi a gun bikin, Mr. Liu Qi, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing ya yi maraba da zuwan 'yan wasa nakasassu da suka zo daga yankuna daban daban na duk duniya da hannu biyu-biyu. Mr. Liu ya ce, Lawal:"Shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta shekara ta 2008 amincewa ce da duniya ta nuna wa kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin da jama'ar Sin suna goyon bayan gasar bisa hasken zukatansu sosai. Kuma bisa bukatar da aka yi kan cewa, shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu mai kayatarwa kamar yadda aka shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing, kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya inganta kayayyaki marasa shinge don yin kokari wajen ba da hidima ta musamman ga 'yan wasa da baki da suka zo daga kasashe da yankuna daban daban. Muna fatan gasar wasannin Olympics ta nakasassu na Beijing za ta zama wani gaggarumin biki wajen morewa da farin ciki da zumunci da buri da kuma nasara. Za mu nuna hasken zukatan Sinawa kan rungumar duniya a gaban duk duniya."

1 2 3 4 5 6 7 8 9