Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Lawal:"Na taba zama zakara a hadaddiyar gasar dunk ta samari ta duk kasar Sin, shiga wasannin Olympics burina ne. Rashin iyawar gani ba ya nuna rashin burina. Ba kawai ya kamata in kawar da wahalhalun da jikina ke kawowa ba, har ma zan karfafa niyyata. Lallai, zan yi iyakacin kokarina, kuma ba zan yi watsi da ko wace gasa ba."

Lubabatu:Wannan magana ta fito daga bakin Li Duan, wato 'dan wasa makaho mafi nagarta na kasar Sin. A gun wasannin Olympics na nakasassu na shekarar 2004 da aka shirya a Athens, ya samu lambobin zinariya guda biyu ga kasar Sin a gun gasar dogon tsalle, da ta tsallen nesa na yin dira 3. Gaskiya ne yana da wuya ga Li Duan da ya samu wannan sakamako mai kyau. Saboda ba ya iya ganin kome, don haka, Li Duan yana gudu, ko yin tsalle bisa tafin da mai horar da shi ya yi. A cikin wannan hali, kullum yana jin rauni.

Lawal:Lallai, ba kawai nakasassu suna bukatar kawar da rashin jin dadi a jikunansu ba, har ma suna bukatar karfafa zukatansu. Shugaban haddadiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin Deng Pufang, wanda ya taba samun lambar yabo ta "Hakkin bil Adam ta M.D.D." ya ce, "Tun farko, wasannin motsa jiki na nakasassu na da ma'anar musamman, nakasassu su kawar da matsalolin da jikunansu ke kawo musu, kuma su tinkari kalubalen wuce iyaka a cikin wasanni a fannonin niyya, da fasaha, da iyawar jiki, kuma su nuna karfin kirkire-kirkire, da darajar dan Adam. A waje daya kuma, ta hanyar wasannin motsa jiki, za a sa kaimi ga warkar da makasassu, da kyautata tunaninsu, da kuma kara karfin zuciya da imani a zaman rayuwarsu, ta yadda za a ciyar da zaman daidai wa daida gaba."

Lawal:Haduwa na matsayin daya daga cikin manyan hasashe 3 da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta yada, ta nuna tunanin wasannin Olympic, wato hada kai da zaman lafiya da kuma jituwa, ya kuma hada da tabbatar da haduwa a tsakanin mutane da a tsakanin mutane da zaman al'ummar kasa da kuma a tsakanin mutane da muhallin halittu.

Lubabatu:Zhang Lianzhi, wani mazauni birnin Tianjin mai shekaru 50 ko fiye da haihuwa, ya dogara da cinikin abubuwan al'adu na tarihi, ya yi shekaru 18 yana ba da taimakon kudi ga nakasssun da suke fama da matsalolin zaman rayuwa. Dalilin da ya sa ya yi haka shi ne domin ruhun 'yan wasa nakasassu ya burge shi sosai, Mr. Zhang ya ce,

Lawal:"Nakasssu su mutane ne masu martaba. Ruhunsu ya burgi mutane sosai. A ganina, taimake su nauyi ne da aka danka wa ko wanenmu, dole ne mu sauke irin wannan nauyi bisa wuyanmu. Ina fatan dukkanmu za mu sami makoma mai kyau."

Lubabatu:A shekarun baya da suka wuce, kasar Sin tana kulawa da nakasassu ta hanyoyi daban daban, ta sami ci gaba sosai wajen raya sha'anin nakasassu. Gwamnatin Sin ta kuma zuba makudan kudade, ta fito da jerin manufofi domin kyautata zaman rayuwar nakasassu da tabbatar da kiyaye iko da moriyarsu. Alal misali, a birnin Beijing, manufofin da aka tsara domin taimakawa nakasassu sun shafi fannoni daban daban na zaman rayuwarsu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9