Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-06 23:39:00    
An bude gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yau da dare

cri

Ya ce, Lawal:"Ina son kallon gasannin Olympic kwarai, a da na kalli gasanni a gida kawai, yanzu filaye da dakunan gasannin Olymic ba su da shinge, zan iya zuwan wurin domin kallon gasanni. Na gaya mutanen da ke makwabtaka da ni da su kalli in ba da kwarin gwiwa ga 'yan wasa a wurin yayin da ake yin gasanni."

Lubabatu:Baya ga filaye da dakunan gasanni, an kuma shirya ayyuka marasa shinge kan fannonin aikin hidima, da masauki, da zirga-zirga domin taimakawa nakasassu ta yadda za su iya jin dadin gasar Olympic kamar yadda mutanen da ba su da nakasa ke yi. A cikin filaye da dakunan gasanni, an kara yin amfani da lifti maras shinge, da na gidajen wanka da na ba haya marasa shinge, da hanyoyin makafi, kuma an kafa tashoshin gyara keken guragu da gabobin na roba, dukkansu sun nuna cewa ana mai da hankali sosai game da 'yan wasa nakasassu. 'Dan wasan kwallon kwando cikin keken guragu na kasar Ukraine viktor Cerpov wanda ya taba halartar gasanni Olympic ta nakasassu uku ya ce, Lawal:"A cikin kwanakin biyu da suka wuce, na je duban dakuna da filayen gasanni, suna da yau sosai, kuma marasa shinge, su dakuna da filaye mafi kyau ne da na taba gani. Ina da sa'a saboda yin gasanni a Beijing."

Lubabatu:Kauyen gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing mai masaukin 'yan wasa da jami'ai ya shirya sosai ga bukatun 'yan wasa kan fannonin cin abinci, da masauki, da zirga-zirga. Kauyen yana da gine-gine 42, kuma ana yin amfani da benaye uku a kasa kasa kawai. Kuma kofa ta ko wane daki ya fi sauran dakunan yau da kullum fadi da kashi 10 cikin 100, an sa makunnin wutar lantarki da marikin kofa kasa kasa. Ban da haka kuma, an mai da hankali sosai wajen shirya dakin wanka. 'Dan wasan jefa faifan karfe na kasar Slovenia Joze Flere ya nuna yabo sosai, ya ce, Lawal:"Ko shakka babu, ana yin aikin hidima da kyau cikin kauyen gasar Olympic ta nakasassu ko yaushe a ko ina. Tabbas ne, aikin hidima a wannan ya kai matsayin taurari biyar. Idan ba ka je wurin ba, ba za ka iya tunanin kyakkyawan halin da ake ciki a wurin ba."

Lubabatu:Ban da haka kuma, yayin da ake gudanar da gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing, za a kebe hanyoyin bos-bos 17, kuma za a yi amfani da bos-bos marasa shinge 400, tare da rukunin motocin taksi marasa shinge. A sa'i daya kuma, an shirya lifti ko na'urorin daukar mutane cikin tashoshin jirgin da ke tafiya a karkashin kasa domin samar da hidima ga nakasassu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9