Lokacin da Beijing ke neman samun iznin shirya wasannin Olympics yau da shekaru 7 da suka gabata, ya yi alkawarin cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta ilmintar da matasa na kasar Sin a fannin wasannin Olympics. Yanzu darussa kan Olympics sun riga sun shafi yara manyan gobe fiye da miliyan 400. Madam Flor Isava-Fonseca, 'yar kasar Venezuela mai shekaru 87 da haihuwa, wadda ta zama memba mai daraja ta kwamitin wasannin Olympics na duniya tana ganin cewa,
Lubabatu: "Wannan wata kyakkyawar dama ce ga kasar Sin, mutane za su ga yadda zamantakewar al'ummar kasar Sin ta samu canji. Kasar Sin ta bude kofa ga kasashe da yankuna 204 na duniya, Sinawa da Turawa da 'yan Afirka da kuma 'yan nahiyar Amurka sun taru ba tare da nuna bambanci ba, kuma sun zama 'yan uwa da kuma aminai. Sabo da haka matasan kasar Sin za su samu moriya sosai a fannonin girman jikinsu da kuma tunaninsu. Kuma wannan shi ne abin tarihi mafi muhimmanci da wasannin Olympics ya bai wa kasar Sin."
Bala: To, masu sauraro, wakar da kuka saurara dazun nan shi ne wata wakar kasar Sin mai taken "zuciyata ta kishin kasar Sin" da kungiyar mawaka ta Kayamba ta kasar Kenya ta rera. Ta haka ana iya gano cewa, ba gasar wasannin Olympics ta Beijing ta amfana wa kasar Sin kawai ba, har ma ta kawo wa duk duniya alheri. A gabannin ko kuma a bayan kaddamar da wasannin Olympics, kwararru kusan dubu 10 a fannin wasan fasaha da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 80 sun taru a Beijing don nuna nagartarrun wasannin fasaha da nune-nune da kuma harkokin al'adu 227, ta haka an inganta cudanya da mu'amala da ke tsakanin al'adu iri daban daban, da kuma kara fahimtar juna da zumunci da ke tsakanin jama'a na kasashe daban daban.
1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
|