Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 23:04:46    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Bala: Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, shirin da kuke saurara shi ne shirin musamman da muka tsara domin bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing?kuma ni ne Balarabe tare kuma da abokiyar aikina, Lubabatu muke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin. Wakar da kuke saurara ita ce wakar wasannin Olympic. A wannan rana da dare, bisa agogon Beijing, wannan waka ta sake fitowa a sararin sama na filin wasannin motsa jiki na kasar Sin, wato "Shekar Tsuntsu". wato ke nan rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi da aka yi kwanaki 16 ana yinsa a nan birnin Beijing.

Lubabatu: Masu sauraro, assalamu alaikum. A cikin wadannan kwanaki 16 da suka gabata, 'yan wasa da suka zo daga kasashe da yankuna 204 shun bayyana mana ruhun Olympic, wato "kara neman sauri da cigaba da kuma karfi", kuma sun bayyana ainihin tunanin Olympic, wato "shiga ya fi samun nasara muhimmanci". Ban da wannan kuma, sun sanya a cimma buri na "duniya daya, mafarki daya" da ake nema a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Lubabatu: A wannan rana da dare, an yi amfani da wani gagarumin biki domin tunawa da wadannan kwanaki 16 da ba za a manta da su ba har abada, kuma an rera wakar shimfida zaman lafiya da sada zumunta.

Bala: A gun bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, Liu Qi, shugaban kwamitin shirya gasar ya bayar da jawabi, inda ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing gaggarumin biki ne na wasannin motsa jiki da ke shimfida zaman lafiya da sada zumunta.

"A cikin kwanaki 16 da suka gabata, 'yan wasa da suka zo daga kasashe da yankuna 204 sun bayyana wa jama'a karfinsu na yin gasanni mafi gwaninta da halin kirki da suke ciki lokacin da suke gasar. Sun kuma samu kyawawan makin da ake alfahari sosai. A waje daya kuma, sun kafa matsayin bajinta na duniya har sau 38 tare da kafa sabbin matsayin wasannin Olympic har sau 85. Gasar wasannin Olympic ta Beijing aminci ne da kasashen duniya suka yi wa kasar Sin. Jama'ar kabilu daban daban da suka zo daga kasashe da yankuna daban daban, kuma suke bayyana al'adu iri iri sun hada kan juna sun kafa wani babban iyalin Olympic. Sun kara samun fahimta da sada zumunci a tsakaninsu. Jama'ar kasar Sin sun cika alkawuransu cike da annashuwa, kuma sun cimma burin shirya wata gasar wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba da yin amfani da fasahohin zamani da yada abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum. Wannan gasar wasannin Olympic ta Beijing za ta kawo mana dimbin abubuwan tarihi na al'adu da na wasannin motsa jiki."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11