Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 23:04:46    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Bala: Bisa bayanin da kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya yi, an nuna wasannin Olympics na Beijing mai halin musamman a fannoni guda hudu, wato mai sigar kasar Sin, da al'adu, da halin zamani, da kuma shigar wasannnin da duk jama'ar kasar ke yi.

Lubabatu: Abin da kuke saurara shi ne, wasan da aka nuna a gun bikin bude wasannin Olympics na Beijing. Gregory Mosher, daraktan cibiyar kirkire-kirkiren fasahohin wasanni ta jami'ar Kolombia ta kasar Amurka, ya darajanta cewa, bikin bude wasannin Olympics na Beijing ya nuna al'adu musamman na kasar Sin, kuma ya nuna ra'ayin "wasannin Olympics na al'adu".

Bala: "Lallai, nuna abubuwa da dama kan al'adun kasar Sin sun faranta ran mutane kwarai da gaske, daga kidan ganguna zuwa wasan da ake kira hanyar siliki da aka nuna a bikin bude wasannin, har zuwa tashin tutar Olympic mai zobba 5, dukkansu sun burge ni sosai, 'yan kallo sun iya sauraran dogon tarihi, da al'adun gargajiya na kasar Sin ta shekaru dubai."

Lubabatu: A hakika dai, ban da bikin bude wasannin Olympics, an kuma bayyana ra'ayin "wasannin Olympics na al'adu" a dukkan wasannin. Kamar misali, tambarin taron wasannin Olimpic, da alamun fatan alheri na yara biyar masu kawo alheri wadanda aka tsamo sifofinsu ne daga kifi da panda da wutar yola na Olympic da bareyi irin Tibet da tsattsewa, da kuma lambobin yabo, da dai sauransu, dukkansu suna hade da sinadaran kasar Sin.

Bala: Bisa alkawarin da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ta yi, matsayi mai kyau na gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kasance a fannoni da yawa, ciki har da ayyukan gina filaye da dakunan wasanni da tsara shirye shiryen wasanni, da bikin bude gasar wasannin Olympics ta aikace aikacen al'adu, da ba da hidima ga kafofin watsa labaru da kula da ra'ayoyin jama'a, da aikin tsaro, da masu aikin sa kai da hidimarsu da dai sauran fannoni. A cikin kwanaki 16 da suka gabata, 'yan wasa da jami'ai, da kuma 'yan yawon shakatawa da suka zo daga kasa da kasa sun ga daguwar matsayin gasar wasannin Olympics da idanunsu. Kakakin hukumar wasannin Olympics ta duniya madam Giselle Davies ta yi jinjina sosai ga ayyukan tsara gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ta ce,

Lubabatu: "Kasar Sin ta gudanar da dukkan ayyukan tsara wasanni da kyau, ciki har da ayyukan karbar gaggan baki da 'yan kallo masu yawan gaske, mun gamsu da hakan."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11