Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 23:04:46    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Lubabatu: Game da gasar wasannin Olympics ita kanta, gasar wasannin Olympics ta Beijing ita ma tana da ma'ana ta musamman. Harkar mika wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing harka ce da ta shafi lokuta da fannoni da kuma mutane mafi yawa a tarihin wasannin Olympics. Ban da wannan kuma, 'yan wasa fiye da dubu goma da suka zo daga kasashe da yankuna 204 sun shiga gasar, manema labaru fiye da dubu 30 sun zo Beijing don yada labarun gasar, kuma jama'a biliyan hudu na duk duniya sun kalli gagarumin bikin bude gasar, dukkan wadannan abubuwa sun zama na farko a tarihin wasannin Olympics, da kuma inganta tasirin da wasannin Olympics ya bayar.

Bala: Jama'a masu sauraro, barka da ci gaba da sauraran shirinmu na musamman game da bikin rufe gasar Olympic ta Beijing daga nan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin, wato CRI.

Lubabatu: Yau da dare, an kashe wutar Olympic ta Beijing. Kuma an mika sanda ta gudanar da wata gasar wasannin Olympic daban ga birnin London na kasar Britaniya. Gasar Olympic ta Beijing, wata musafaha mai babbar ma'ana da aka yi tsakanin gasar Olympic mai dogon tarihi da al'adu masu nagarta na al'ummar Sin, kuma wata musaya da aka yi tsakanin al'adun kasashe dabam daban na duniya da al'adun kasar Sin, kuma wata tattaunawar da aka yi tsakanin al'adun yamma da na gabas. Kwanaki 16 na gasar Olympic ta Beijing ba tsawon lokaci ba, amma amincin da aka samu a cikin wadannan kwanaki 16 zai kasance cikin dogon lokaci. Daga duk inda ka fito, kuma duk inda za ka tafi, dukkanmu mu zama tamkar iyali har adaba.

Bala: Yau da dare, bari mu zuba ruwa a kasa mu sha, yau da dare, bari mu yi alkawarin sake saduwa da juna a gun gasar Olympic ta London a shekara ta 2012 saboda duniya daya, mafarki daya. Sai mu sake saduwa da juna bayan shekaru 4!


1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11