Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 23:04:46    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Bala: Jama'a masu sauraro, shirin da kuke saurara shi ne shirin da gidan rediyon kasar Sin, wato CRI ya tsara domin bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing musamman.

Lubabatu: "Kara neman sauri da cigaba da kuma karfi" ainihin ruhu ne na wasannin Olympic. A cikin kwanaki 16 da suka gabata, an fitar da lambobin zinariya 302 a gun gasanni iri daban daban na wasannin Olympic na Beijing, kuma an karya matsayin bajimta na duniya da na wasannin Olympic har sau da yawa.

Bala: A ran 13 ga watan Agusta da yamma, madam Liu Chunhong ta kasar Sin ta samu wata lambar zinariya a gun gasar wasan daga nauyi na matsayi mai nauyi kilo 69, kuma har sau 5 ta karya matsayin bajimta na wannan wasa.

Lubabatu: "A gun gasar wasannin Olympic ta Athens ta shekara ta 2004, ban daga nauyi ba a zagaye na karshe. Sabo da haka, lokacin da na samu nasarar daga nauyi na karshe a gun wannan gasa, ina cike da jikuwa sosai, kamar zan yi kuka. Na gano ban bata wadannan shekarun da suka gabata ba."

Bala: A gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'yan wasa masu dimbin yawa sun karya matsayin bajimta da yawa. Alal misali, a cikin gasar harbe-harbe ta mata ta zangon mita 10, Katerina Emmons ta kasar Czech ta karya matsayin bajimta na wannan wasa, kuma ta samu lambar zinariya ta farko ta gasar wasannin Olympic ta Beijing. A cikin gasar iyon rigingine ta mata ta zangon mita dari 2, Kirsty Coventry, 'yar wasa ta kasar Zimbabwei ta karya matsayin bajimta kuma ta samu wata lambar zinariya. Ita kuma ta zama 'yar wasa ta farko ta Afirka da ta samu lambar zinariya a ciki gasar iyo a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. Lubabatu: A waje daya kuma, a gun gasar harbe-harbe ta maza ta zangon mita 10, Abhinav Bindra na kasar Indiya ya samu wata lambar zinariya, wato lambar zinariya ta farko da kasar Indiya ta samu a gun gasannin wasannin Olymic. Dukkan kasashe da yankunan da suka shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing sun samu sakamako mai kyau a gun wannan gasa. 'yan wasan kasar Sin, wato mai masaukin gasar sun yi kokarin ka'in da na'in sun samu cigaba a gasanni da yawa. A sakamakon kokarinsu, a karon na farko ne kasar Sin ta hau kan mukami na farko a kan dakalin yawan lambobin zinariya na wasannin Olympic, wato ta samu maki mafiya kyau bayan da ta shiga gasannin wasannin Olympic.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11