Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 23:04:46    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Bala: "Lambar zinariya da aka samu za ta raka ka har abada, wato za ka zama mai samun lambar zinariya ta gasar wasannin Olympic har abada. Ina ganin cewa, kowace shekara, na kan taya murnar haihuwa da kirismeti, amma idan ina son zama zakaran gasar wasannin Olympic, to, sai bayan shekaru hudu."

Lubabatu: Wannan shi ne ra'ayin shiga gasa da 'dan wasan iyo daga kasar Amurka Michael Phelps ya nuna mana bayan da ya gama gasannin da aka shirya. A gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, gaba daya Phelps ya samu lambobin zinariya 8, da haka ya zama 'dan wasa wanda ya fi samun yawan lambobin zinariya a tarihin gasar wasannin Olympic, sunansa zai kara yaduwa a duk fadin duniya tare da gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Bala: "Na san na karya matsayin bajimta na duniya bayan da na gama gasa, ina jin dadi sosai da sosai saboda na samu zama na farko na gasar wasannin Olympic."

Lubabatu: Muryar nan ta fito ne daga bakin 'dan wasan kasar Jamaica Usain Bolt. A ran 16 ga wata, Bolt ya karya matsayin bajimta na duniya da dakika 9 da 69 a gun gasar karshe ta gudun mita 100 na maza, wato ke nan a karo na farko ne dan adam ya kashe lokacin da bai kai dakika 9 da 70 ba wajen gasar gudun mita 100. Wannan sakamakon zai hadu tare da gasar wasannin Olympic har abada.

Lubabatu: Masu sauraro, barka da ci gaba da sauraran shirin musamman da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ke gabatar muku kan bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Bala: 'Yan wasa sama da dubu goma sun yi takara domin neman samun lambobin zinariya 302, shi ya sa kalilan dake cikinsu kawai sun samu lambobin zinariya da sauran lambobin yabo. Amma 'yan wasa daga kasashe da shiyyoyi daban daban sun nuna kwazo da himma wajen shiga gasannin saboda suna so su nuna mana tunanin wasannin Olympic wato "shiga gasa ya fi cin nasara muhimmanci", ana iya cewa, dukkan 'yan wasa jarumai ne a gun gasar wasannin Olympic.

"Iraki! Iraki! Iraki!"

Lubabatu: Yayin da 'yan wasa 7 daga kasar Iraki suka sauka nan Beijing a lokaci na karshe domin shiga gasar wasannin Olympic, sai 'yan kallo suka yi ihu da babbar murya domin maraba da zuwansu. Jami'in kula da harkar wasannin Olympic na kasar Iraki Sarhad Fatah ya gaya mana cewa, "Yan jarida da jama'a na kasar Sin da sauran kasashen duniya suna mai da hankali kan kungiyar 'yan wasan kasar Iraki. Ko da yake Iraki tana cikin hali mai tsanani yanzu, amma 'yan wasa sun daidaita wahalhalun dake gabansu sun yi atisaye kuma sun shiga gasa a madadin kasarmu. Jama'ar kasar Iraki suna alfahari dominsu, jama'ar kasashen duniya su ma sun nuna yabo gare su."

Bala: Rubina Muqimyar ita ce mace daya kadai dake cikin kungiyar 'yan wasan kasar Iraki, a ganinta, ta riga ta cimma burinta saboda ta samu iznin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Lubabatu: "Na hakkake cewa, zan ci nasara a gun wannan zama na gasar wasannin Olympic, shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing shi ne buri mafi muhimmanci a cikin rayuwata, yau ma na riga na cimma burina."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11