Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 23:04:46    
An rufe gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta lokacin zafi a nan birnin Beijing

cri

Shugaban kwamitin daidaita ayyukan shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing daga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Mr. Hein Verbruggen ya yaba wa ayyukan ba da hidima ga kafofin watsa labaru a yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ya ce,

Bala: "Babbar cibiyar watsa labarai ba wani wuri ne da manema labaru suke aiki kawai ba, har ma ta zama gida ta biyu a gare su. Sun yi aiki a dukkan awoyi 24 na ko wace rana a wurin, domin watsa labaru daban daban ga jama'a. Ya kamata mu nuna godiya ga hukumomin da suka kula da harkokin babbar cibiyar watsa labarai, sun biya dukkan bukatun manema labaru, cikin nasara, sun mayar da wurin da ya zama wani gida na kafofin watsa labaru daga kasa da kasa."

Wata 'yar yawon shakatawa daga kasar Australiya madam Bulinda ta nuna amincewa sosai ga masu aikin sa kai. Ta ce,

Lubabatu: "Masu aikin sa kai suna da yawa, suna da himma kuma suna son taimakawa saura. Sun bayyana mana hanyoyin gaskiya, sun ba mu laima a yayin da ake ruwan sama. Dukkan wadannan abubuwa sun faranta raina, masu aikin sa kai suna da abokantaka. "

Lubabatu: Jama'a masu sauraro, yanzu kuke sauraran shirin musamman na bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing daga gidan rediyon kasar Sin.

Bala: Cimma burin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing da ke da abubuwan musamman da daguwar matsayi, ba za a iya raba shi da ra'ayoyi uku ba wato wasannin Olympics na kyakkyawan muhalli, da wasannin Olympics na kimiyya da fasaha, da kuma wasannin Olympics na al'adu.

Lubabatu: Tun bayan da birnin Beijing ya ci nasarar neman damar shirya gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008 a shekarar 2001 har zuwa yanzu, birnin Beijing ya zuba kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 140 wajen kiyaye muhalli. A halin yanzu dai, birnin Beijing ya riga ya cika dukkan alkawuran da ya dauka a yayin da yake neman izinin shirya gasar wasannin Olympics. Ra'ayin wasannin Olympics na kyakkyawan muhalli ba ma kawai ya kara samar da sararin samaniya mai launin shudi, da tsabataccen ruwa kawai a birnin Beijing ba, har ma zai iya dasa ra'ayin kare muhalli a cikin zuciyar jama'a. Jakadan kasar Tanzaniya da ke kasar Sin Mr. Omar Mapuri ya bayyana cewa,

Bala: "A halin yanzu, ingancin iskar Beijing ya kara samun kyautatuwa, wannan dai ya faru ne sakamakon matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka a jere wajen tabbatar da ingancin iska. Isowata a birnin Beijing, da na sauko daga jirgin sama, sai na ga itatuwa da yawa da aka dasa a gefunan hanyoyi, na ji dadi sosai domin hakan, a cikin birnin Beijing kuma, akwai itatuwa da yawa kamar haka."

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11