Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 17:16:12    
Sharhohi daga masu sauraron kasashen duniya kan batun Tibet

cri

Muryar Asiya:Muna fatan kallon wasannin Olympics cikin farin ciki, a maimakon nuna karfin tuwo da ake kyamarsu

Anand Mohan, wani mai sauraron gidan rediyon kasar Sin daga jihar arewa ta kasar Indiya, ya buga wayar tarho ga tashar internet ta harshen Indiya ta gidan rediyon kasar Sin cewa, "aukuwar tarzoma a yankin Tibet ta ba ni mamaki. Daga shafinku na internet, na san cewar, gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da Sin ta yi sun kawo wa jama'ar Tibet babban alheri, zaman rayuwar jama'a ya kara ingantuwa, musamman ma hanyar dogo da aka fara aiki da ita ba da jimawa ba a tsakanin Tibet da Qinghai ta hau da wata gada ta yin musanyar kayayyaki da cudanyar jama'a a tsakanin Tibet da sauran yankuna daban daban na kasar Sin, kuma karin jama'a sun isa wannan kyakkyawan wuri na Tibet bisa wannan hanyar dogo. Tibet a hade take da kasarmu Indiya, shi ya sa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Tibet na shafar zaman lafiyar Indiya da cigabanta, ina Allah wadai da tarzomar da ta auku a Tibet, wadda aka tayar da ita ba tare da kulawa da zaman lafiya ba, kuma ina fatan ba za a samu karin irin wannan al'amura ba."

Internet bai bunkasa sosai ba a kasar Nepal, amma duk da haka, akwai masu karanta shafunan internet da suka rubuto wa tashar internet ta harshen Nepal ta gidan rediyon kasar Sin cewa, suna jin fushi sosai dangane da ayyukan nuna karfin tuwo da rukunin Dalai Lama suka yi na lalata cigaban Tibet, kuma sun nuna tsayayyen goyon baya ga manufar Sin daya tak a duniya.

A cikin sakonsa, Musa Ozal, wani mai karanta shafin internet na harshen Turkiya na gidan rediyon kasar Sin ya ce, "daga shafinku na internet, na sami gaskiyar al'amarin. Na yi bakin ciki sabo da lalata kwanciyar hankali a Tibet da wasu 'yan tawaye suka yi. Ina nuna goyon baya ga matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka. Al'amarin da ya auku a Tibet shiri ne da aka tsara sosai, a maimakon wani abu na ba zata. Wasannin Olympics kasaitaccen biki ne da ni da abokaina muka dade muke zura ido a kansa, kuma dukanmu na fatan kallon wasan cikin farin ciki, a maimakon nuna karfin tuwo da ake jin kyamarsu.

Masu karanta shafunan internet da suka zo daga kasar Iran sun buga waya ko aika da Email ga tashar internet ta harshen Farisa na gidan rediyon kasar Sin, inda suka nuna kulawa ga aukuwar tarzoma a Tibet, kuma suka nuna goyon baya ga matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka.

A cikin sakon Email da Saed Rahman, wani mai karanta shafunan internet daga kasar Afghanistan, ya aika ga tashar internet ta harshen Pushtu ta gidan rediyon kasar Sin, ya ce, "ban fahimci me ya sa wasu mutane suka hada batun Tibet da wasanin Olympics na Beijing, ina imanin da cewa, Sin na iya gudanar da wasannin Olympics yadda ya kamata, kuma ina sa rai sosai, kuma ba shakka zan kalli wasannin." Mai sauraro Lafwra Mandusher har ya buga waya ga ma'aikatan sashen Pushtu cewa, "daga shafinku na internet da rediyonku, na sami cikakkiyar fahimta dangane da al'amarin, abin da nake so fada kawai shi ne, babu ko shakka, Tibet wani kashi ne na kasar Sin! Ku ci gaba da kokarin aiki, zan zuba muku ido har kullum."


1 2 3 4 5 6 7