Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 17:16:12    
Sharhohi daga masu sauraron kasashen duniya kan batun Tibet

cri

Murya daga Turai: sannu sannu ne ba cikin sauri ba, kasashen Turai sun amince da labaran da suka bayar ba bisa gaskiya ba.

Mai karantawa Mr Giuseppe na kasar Italiya ya taba zuwa birnin Lhasa. Ya ce, 'na taba zuwa birnin Lhasa a shekarar 2007, mazaunan wurin suna zaman rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, zaman rayuwarsu kuma ya samu kyautatuwa sosai. Na taba zuwa jihar Tibet har sau uku, na ga ingantattun hanyoyin mota da aka gina, birane sun kara kyaun gani. Ina bakin cikin sosai, domin lamarin laifuffukan duke-duke, da fasa kayayyaki, da kwashe kayayyakin jama'a, da cunnama wurare wuta ya lalata zaman karko a Tibet. Sabo da haka ne, da babbar muriya ce, na yi adawa da lamarin nuna karfin tuwo ga farar hula. Ina jiran sake kai ziyara a jihar Tibet ta kasar Sin, ina so in sake ganin kwanciyar hankali a wurin.'

Mr Bernd Kolkwitz na kasar Jamus ya rubuto wata wasika ga tashar internet ta harshen Jamusanci ta CRI cewa, 'abin bakin ciki gare ni shi ne, ya kasance da mutane masu baki biyu a kasar Jamus. Ga kasashen waje, sun ce sun amince da cikakken yankin kasar Sin, amma a gida na kasar Jamus, sun gudanar da manufofin da ke da bambanci sosai. A 'yan kwanakin baya, wasu kafofin watsa labaru na kasar Jamus sun yi amfani da lamarin da ya faru a jihar Tibet ta kasar Sin, su shiga tsakanin lamarin, domin a yi adawa da gurguzu a kasar Sin, haka kuma suna neman yin amfani da lamarin da ya zama wata hujjar adawa da gasar wasannin Olympics ta Beijing.'

Mr Lee na kasar Jamus ya rubuta bayanai kan shafin internet na tashar internet ta harshen Jamusanci ta CRI cewa, 'a 'yan kwanakin baya, wasu kafofin watsa labaru na kasar Jamus ciki har da N-TV, da ARD, da ZDF da kuma Der Spiegel da dai sauransu sun bayar da labarai dangane da lamarin Tibet ba bisa gaskiya ba, sun yi karya ba tare da jin kunya ba. Idan irin wannan abu ya faru ne kafin shekaru 50, mai yiyuwa ne ba a san abin da suka yi karya ce, amma a zamanin yau, tabbas ne za su yi da-na-sani. Ina fatan mutane da yawa za su kara ganin labarai daga tashar internet ta CRI.'

Mai saurarommu Mr Mirko L ya rubuta wata wasika gare mu cewa, 'a 'yan kwanakin baya, an yi ta mai da hankali sosai kan lamarin da ya faru a jihar Tibet ta kasar Sin. A ganina, hukumomin leken asiri da kuma rukunoninsu na kasashen waje sun yi kulle kullen lamarin ne, tare da makasudin kawo wa kasar Sin rikicin siyasa a shekarar gasar wasannin Olympics, da yadda za su iya kebantar da kasar Sin a duk duniya. Ina fatan gwamnatin kasar Sin za ta sarrafa halin da ake ciki tun da wuri, kada kasashe masu nuna fin karfi su cimma makircinsu na sanya kasar Sin cikin rikici.'

1 2 3 4 5 6 7