A 'yan kwanakin baya, bayan da tashoshin internet na Gidan rediyon kasar Sin wato CRI sun bayar da lamarin Tibet cikin harsunan da yawansu ya kai 39, masu karantan shafinmu na internet sun rubuta bayanai kan shafin internet, da rubuta wasikoki, da kuma buga wayar tarho, domin mayar da martani kan lamarin. Ga wasu daga cikinsu.
Sharhi daga masu sauraron kasashen Afirka: muna fatan kasar Sin za ta shirya wata gasar wasannin Olympic da kyau, sakamakon haka, abokan gabanmu za su ci mutunci
A ran 7 ga wata, malam Mamane Ada, wani dan kasar Nijar wanda ke saurarar shirye-shiryen sashen Hausa na CRI ya aiko mana wata wasika, inda ya ce, "yau ne gwamnatin Nijar ya fido wata sanarwa dake da nasaba da abun a'asha daya wakana a birnin Lhasa mai cin gashin kansa na kasar Sin. A dunkule gwamnatin Nijar ya ce haka: Gwamnatin kasar Nijar ya sa ido cikin damuwa kan abubuwan da suka apku a binin Lhasa na jahar Tibet mai cin gashin kanta, sanarwar ta cigaba da cewa wannan tashe tashen hankalin sun hadasa lalacewar kayayaki masu yawa har ma da mutuwar mutane?hakan kuma ya kawo rudani a jihar ta Tibet dalilin haka kuma shi ne na kawo rauni ga kokari da fadi ka tashin da kasar Sin ke yi domin shirye-shiryen wasannin Olympics na Beijing a watan Agusta na 2008. A game da wannan ne 'yan Nijar tare da sunan shugaba Tanja Mamadu sun yi Allah waddai da wannan al'amri kuma suke kawo goyon baya ga hukumomin kasar Sin da jama'ar su."
A waje daya kuma, a cikin wasikar da malam Salisu Dawanau na kasar Nijeriya ya rubuta wa shafin yanar gizo na harshen Hausa na CRIonline, ya ce, "Cikin kwanakin nan, Duniya ta saurari labarin abubuwan da suka faru a Tibet ta kasar Sin. A nawa ra'ayin, wannan abu ne na cikin gida da ya shafi kasar Sin, kuma kasar ce kawai ta san hanyoyin da zata bi na ganin ta tabbatar da tsaron kasarta da kuma samun kwanciyar hankalin mutanen kasarta.
Alal hakika, na saurari kafofin yada labarai daban-daban na kasashen Duniya, kuma na ji ra'ayoyin mutane game da wannan batu mai sarkakiya. A zahirin gaskiya, lamarin yana da nasaba da siyasar Duniya, don haka bai kamata mutane su yi katsalandan a ciki ba. Kowace kasa dai tana da nata matsalolin, saboda haka idan ba za'a taimaka wa kasa yadda zata fita daga matsala ba, to bai kamata a yi abinda zai lalata kasar ba.
Abin al'ajabi, wasu kasashen Turai da na Yammaci suna yada farfaganda maras-asali, suna danganta waccan al'amari na Tibet da halarcin wasannin gasar olympic wadda kasar Sin zata dauki nauyin shiryawa a wannan shekara ta 2008.
Abin tambaya shi ne, shin wadannan kasashe na yi wa kasar Sin adalci ke nan?
Duniya dai bata manta da irin yadda kasar Amurka, tare da 'yan kazaginta, suka farma kasashen Afghanistan da Iraq da yaki ba. Muna sane da irin take hakkin dan-Adam da ke aukuwa a Turai da kuma kasashen Yammaci. Muna sane da zalunce-zalunce da ake yi a wadannan kasashe. Muna sane da yadda wadannan kasashe, saboda fin-karfi, ke tursasa wa wasu kasashe masu tasowa musamman na Afirka don haddasa fitina da tashin-hankali da kuma yake-yake don su cimma kudurorinsu ta hallaka mutane masu dumbin yawa.
Masu iya magana kan ce, "komai nisan dare, gari zai waye". Kuma "karya, fure take bata 'ya-'ya". Manufa a nan shi ne, kwanci-tashi idanun mutanen Duniya zai bude ta yadda duk zamu rungumi gaskiya, mu kuma yi amfani da ita.
A karshe, ina yin kira da babbar murya ga kasashen Duniya da su yi niyyar zuwa kasar Sin domin halartar gasar wasannin olympic ta bana don gane wa idanunsu abubuwan ban sha'awa da mamaki game da kasar Sin. Su kuma gane wa idanunsu gasar olympic irin wacce ba'a taba yi ba a duk tarihin gasar da aka yi a can baya. Jama'a, mu yi hattara, kada a yi mana "sakiyar da babu ruwa". Daga kin gaskiya dai, sai bata."
A cikin wasikar da Mr. Idris Buwadina, wani mai karanta shafin yanar gizo na sashen Larabci na gidan rediyon kasar Sin ya rubuta, ya ce, "kasar Sin kasa ce da ke da tarihi da al'adu na dogon lokaci. Wannan gasar wasannin motsa jiki ta Olympic tana da muhimmanci sosai a gare ta. Yanzu dukkan kasashen duniya suna zura idanunsu kan birnin Beijing. Muna kuma fatan za a kaddamar da wannan gasa lami lafiya kamar yadda ya kamata. A waje daya kuma, gasar wasannin motsa jiki ta Olympic kasaitaciyar gasa ce ta duk duniya. Duk wadanda suke yunkurin lalata gasar Olympic gwagwarmayar da suke yi da duk duniya, su kuma abokan gabanmu ne domin muna son kasar Sin. Abin farin ciki shi ne, gwamnatin kasar Sin da gwamnatin jihar Tibet sun riga sun yi kokari tare wajen tabbatar da kwantar da tashe-tashen hankali da aka yi a birnin Lhasa, yanzu kuma an riga an samu kwanciyar hankali a birnin.
Mr. Idris ya kara da cewa, "mu ma kasa ce mai bin addini, addinin da muke bi yana da tsarki kwarai. Ana bukatarmu da mu yi kokari tare wajen neman jituwa a zaman al'umma da tabbatar da kwanciyar hankali a wata kasa har ma zaman lafiya a duk duniya."
Mr. Ben Amir Aid, wani dan kasar Aljeriya wanda yake saurarar shirye-shirye da karanta shafin yanar gizo na sashen Larabci na CRI ya kuma rubuta wasika, cewar "ana bacin rai sosai domin matsalar nuna karfin tuwo da aka yi a birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin. Mai yiyuwa ne wannan sakamako ne da wasu mutanen kasashen waje wadanda suke yunkurin kawo wa kasar Sin baraka suka yi bisa shirin da suka tsara. Suna son bata sunan kasar Sin ta hanyar tayar da irin wannan matsala, musamman a jajibirin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta shekarar 2008. Kowace kasa, ciki har da kasar Sin tana da ikon daukar matakan da suka dace a idanunsu wajen daidaita irin wannan matsalolin nuna karfin tuwo da rikice-rikicen da suke kawo illa ga halin kwanciyar hankali da take ciki. Wannan kuma harkokin cikin gida ne na kowace kasa, sauran kasashen duniya ba su da ikon sa hannunsu a ciki."
Mr. Fadhili Kipene, wani mai sauraron sashen Kiswahili na CRI daga kasar Tanzania ya rubuta wata wasika, cewar "lokacin da nake saurarar shirye-shiryen sashen Kiswahili na gidan rediyonku, na gane cewa, miyagun laifuffukan da tsirarrun mutane suka yi a jihar Tibet sun kawo illa ga zaman rayuwar jama'a da dukiyoyinsu na wurin. Ina da imanin cewa, wadannan miyagun laifuffuka ne na bakin ciki, tabbas ne za su sha kaye. Ina ganin cewa, rukunin Dalai da ke gudu hijira a kasashen waje ne ya dade yana shirya irin wadannan miyagun laifuffuka. A waje daya kuma, sun samu goyon baya daga tsirarrun mutane na kasashen waje. A watan Janairu na shekarar 2007, na taba karanta wata mujella ta VOA, inda aka buga wani dogon bayanin da ke tattaunawa kan batun Tibet. Har ma wanda ya rubuta wannan bayani ya ce, yana goyon baya ga rukunin Dalai da ya nuna adawa da ikon mulki da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa a jihar Tibet, kuma a kebe yankin Tibet daga yankunan kasar Sin, har ma a kafa wata haramtaciyyar gwamnati a Tibet. Ina ganin cewa, tsirarrun mutanen wasu kasashen yammacin duniya ne suke sa kaimi kan wasu 'yan Tibet da su dauki matakai iri iri domin lalata gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta 2008 da za a yi a birnin Beijing, da kuma lalata babban sakamakon da kasar Sin ta samu a fanning tattalin arziki bayan da ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen duniya."
Mr. Mchana J Mchana, wani dan kasar Tanzania daban wanda yake sauraran shirye-shiryen sashen Kiswahili na CRI ya kuma turo mana wasika ta E-mail, cewar "Ina rokonku da ku wakilce ni ku gai da jama'ar Lhasa wadanda suka samu harasar zaman rayuwarsu da dukiyoyinsu a cikin matsalar nuna karfin tuwo da aka tayar a kwanan baya a birnin Lhasa. Bayan da na samu wannan labari, ina bacin rai sosai, domin wannan hasara ce ta dukkan dan Adam na duk duniya. Wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun kuma taka rawarsu a cikin wannan matsala, wannan ya shaida cewa, sun riga sun halarci wannan matsala kai tsaye, kuma suna sa kaimi kan wadannan mutanen da suke yunkurin kawo wa kasar Sin baraka. Rukunin Dalai yana gudun hijira a sauran kasashen duniya, ina tsammani shi ne ya tsara shirin tayar da wannan matsala a birnin Lhasa. Wasu mutane sun samu daga hannunsa, ya kuma yi amfani da su da su kasance kamar kayan aiki na tayar da wannan tashin hankali. Bayan da wasu mutane sun karbi kudi, za su iya yin abubuwan da ake nemansu da su yi, har ma za su iya sanar da iyayensu. Dole ne shugabanni da jama'a na kasar Sin su yi hadin guiwa kamar wani babban dutse wajen sarrafa halin da ake ciki a birnin Lhasa. A hakika dai, yanzu wasu tsirarun mutane ba su son ganin kasar Sin ta shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing cikin halin kwanciyar hankali cikin lumana. Ina fatan kada jama'ar kasar Sin su bace ransu, kuma za su iya ci gaba da shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing bisa shirin da ta tsara. Sabo da haka, abokan gabanmu za su ci mutuncinsu."
1 2 3 4 5 6 7
|