Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 17:16:12    
Sharhohi daga masu sauraron kasashen duniya kan batun Tibet

cri

Ran 27 ga wata, Gerardo ya aiko mana sako daga kasar Nicaragua, inda ya kai suka da kakkausar murya ga laifin da Dalailama ya yi. Ya ce: "Idan gunki mai kirki ya ga laifinsa, ko shakka babu zai kai shi zuwa gidan azaba saboda laifinsa ya saba wa ka'idar 'soyayya da zaman lafiya'. Al'amarin da ya auku a ran 14 ga watan Maris yana nufin canja matsayin Tibet zuwa wata jiha ta kasar Amurka. Kuma abin bakin ciki shi ne a kasarmu wato kasar Nicaragua, ba a watsa labaran da abin ya shafa bisa hakikanan abubuwa ba. A kullum akwai wasu mutane wadanda ba su son ganin wadatuwar kasa, har ma suna lahanta zaman karko da suna na kasa. Ana iya cewa, suna yin amfani da lamarin don nuna kiyayya ga gasar wasannin Olympic da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008."

Ricardo Santos daga kasar Brazil ya ce: "Game da hargitsin da ya faru a jihar Tibet ta kasar Sin a ran 14 ga watan Maris na bana, na ji bakin ciki kuma na yi fushi. A ganina, Dalailama shi 'dan siyasa ne kuma shi 'dan ta'adda ne, yana fatan zai cim ma burinsa, amma bai kamata ba ya yi haka ta hanyar saba wa doka. A cikin hargitsin, mutane da yawa da ba su ci ba su sha ba sun rasa rayukansu, kwanciyar hankalin zaman al'umma shi ma ya shiga halin rudani, wannan ya kawo mugun tasiri mai tsanani ga zaman al'ummar kasa. Dukkan wadannan sun nuna mana cewa, rukunin Dalai yana nuna kiyayya ga gwamnatin kasar Sin kuma yana nufin neman 'yancin kan Tibet ta hanyar kuskure. Amma na hakake cewa, za a warware matsalolin dake gabanmu, tabbas ne gwamnatin kasar Sin za ta daidaita halin yadda ya kamata, kuma za a gudanar da gasar wasannin Olympic a watan Agusta lami lafiya. "

Eduardo Caetano daga kasar Brazil ya ce: "Hargitsin da ya auku a ran 14 ga wata ya nuna mana cewa, rukunin Dalailama yana nufin jawo baraka ga kasar Sin, shi ya sa na tsaya tsayin daka na goyi bayan matsayin gwamnatin kasar Sin da matakan da ta dauka kan wannan. Tun tuni, jihar Tibet wani kashi ne na kasar Sin da ba za a iya balle shi daga kasar Sin ba. Bai kamata ba a nuna shakka ga shi, kuma ba za a canja hakinanin abun nan ba har abada."

1 2 3 4 5 6 7