Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 17:16:12    
Sharhohi daga masu sauraron kasashen duniya kan batun Tibet

cri

Ra'ayoyi daga nahiyar Amurka ta kudu da ta tsakiya: Allah ko shakka babu zai yi watsi da abubuwan da suka faru zuwa Wuta.

Mr. Ricardo Huerta mai sauraronmu daga kasar Argentina ya taba kawo ziyara sau biyu ga kasar Sin. A ran 22 ga watan Maris yayin da yake yin ziyara a sashen Spainish na gidan rediyonmu ya ce, "Ina jin fushi sosai kan aikace-aikacen neman ballewar kasar Sin da wasu 'yan neman 'yancin Tibet suka yi. Halin da ake ciki da martanin da kasashen duniya suka mayar sun shaida cewa, ko shakka babu tashe-tashen hankulan da aka yi domin mugun nufi wanda ya karya dokar duniya za su sha kaye."

Mr. Ricardo ya ce, bisa abin gaskiya da ya gani da idanunsa yayin da yake yin ziyara a kasar Sin har sau biyu, wasu mutane sun watsa labarai da ba su da shaida kan halin da kasar Sin ke ciki, kuma suka kawo rudani tsakanin gaskiya da karya.

Mr. Rubens Pedroso mai sauraronmu daga kasar Brazil ya aiko mana wasika cewa, "kullun ina mai da hankali kan al'amarin Tibet ta hanyar dudduba tashar Internet na sashen Portugal na gidan rediyon kasar Sin, wato CRI. Bayan na kalli Vedio na abin da ya faru a birnin Lhasa, da wuya za a iya yarda da manyan laifuffuka masu tsannani sosai da Dalai Lama ya yi. Da ma ina tsamanni shi wani mutumin kirki ne. Ina tsammani, matakain da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun yi daidai kuma cikin lokaci. Ina fatan mutanen da suka gamu da mummunan tasiri a zukatansu za su sami sauki da sauri, kuma ina fatan Dalai Lama zai gane kuskure da manyan laifuffukan da ya yi, da kuma kammala wannan al'amari mai bakin ciki."

Mr. Jhon Freddy Castirllon mai sauraronmu daga kasar Colombia ya rubuta maganarsa a tashar Internet ta CRI cewa, "ina jin bakin ciki ga al'amarin ta da manyan laifuffukan da ya faru a birnin Lhasa, da illar da wannan al'amarin ya yi wa kasar Sin. Ba na son ballewar kasar Sin."

1 2 3 4 5 6 7