Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-08 17:16:12    
Sharhohi daga masu sauraron kasashen duniya kan batun Tibet

cri

Wani mai sauraronmu na kasar Uruguay Mr Alberto Machado ya aiko mana wasika ta hanyar Internet, a daidai ranar da babban taron Majalisar Wakilan Jama'ar Kasar Sin ya yi bikin rufewa a ranar 18 ga watan Maris, inda ya kai suka kan tsirarrun 'yan arewa saboda sun haddasa lamarin yin duke-duke da kwace da fashi da kuma kone kayayyaki a Tibet. Mr Arberto ya rubuta cewa, bisa matsayina na tsohon mai sauraron gidan rediyon kasar Sin wato CRI, ina mai da hankali sosai ga kasar Sin, ba za mu dimauta ba bisa sakamakon jawabin karyar da suka yi .Mu ba za mu manta da cewa, jihar Tbiet ita ce wani tsarkakken yankin kasar Sin, kuma mu ba za mu iya manta da zaman rayuwar da mutanen wurin suka yi kafin 'yantar da Tibet. Mun sani sosai cewa, bisa tsarin yin mulki kan bayi da aka yi a wancan lokaci, wasu tsirarrun iyayengijin bayi sun yi zaman jin dadi sosai bisa sakamakon zubar da jini da hawaye na dimbin bayi manoma, amma bayi manoma da suka zama a matsayin kasa kasa sosai an kwace musu sharudan zaman rayuwa na tushe da mutumci. A wancan lokaci, tattalin arziki na Tibet ya yi baya baya, kuma al'adunta sun tabarbare, kuma an kasa matakai da yawa a tsakanin mutane a zamnatakewar al'umma, jama'ar farar hula su ne suka kasance cikin jahilci. Amma, yanzu, Bisa tsarin aiwatar da harkokin kabilu na kansu a jihar, bisa kulawa sosai da gwamnatin kasar Sin ta yi da goyon baya da dukkan jama'ar kasar Sin suka yi ne, jama'ar Tibet su da kansu suna tafiyar da harkokinsu na kansu sosai, suna raya sha'anin kiwon dabbobi da sha'anin noma da yawon shakatawa. Yaransu suna iya samun damar shiga jami'o'i, sa'anan kuma sun sami girmamawa sosai wajen addini da al'adu da tsabi'u da sauran fannoni. Muna ganin cewa, a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wakilan da suka zo daga jihar Tibet da sauran wakilan kananan kabilu sun yi jawabai yadda suka ga dama, sun ba da dabara da manufa ga bunkasa kasa. Wannan ba abu ne da aka iya yi a zamanin da ba, ina fatan Tibet za ta kara kyau sosai gobe.

Mr Alberto ya ci gaba da cewa, rukunin Dalai ya kulla makircin haddasa hargitsi a Tibet ta yadda jama'ar kabilar Tibet da jama'ar kabilar Han sun yi hasara sosai wajen rayuka da dukiyoyi, an kashe jama'ar farar hula, kuma an kone shaguna ko lalata su, har ma an kai wa likitoci da masu aikin jiyya hari, wannan ne laifin da suka yi. A kodayaushe Tibet ita ce tsarkakken yankin kasar Sin. Ina nuna girmamawa ga gwamnatin kasar Sin saboda kokarin da ta yi na kwantar da hargitsin da kiyaye kwanciyar hankali a Tibet, kuma ina nuna jejeto ga 'yan kasar Sin na kabilar Tibet da kabilar Han wadanda suka sha barna sosai a cikin lamarin nan na duka da kwace da fashi da kuma kone kayayyaki

1 2 3 4 5 6 7