Mai sauraronmu daga kasar Jamus Helmut Matt ya rubuto mana wani e-mail kan wannan batu. Inda ya ce, "Tun daga farko sai na gane, wannan ne matakin da wasu mutanen da ke da nufin hana wasannin Olympic na Beijing da za a shirya ba da dadewa ba. An yada maganganun da labarun da ba na gaskiya ba ne kan lamarin a dukkan duniya cikin sauri, ta yadda ana iya ganin cewa, masu jagorancin lamarin sun shirya sosai. Wasu mutane na kasashen duniya, ciki har da na kasar Jamus, suna adawa da kasar Sin, kuma suna goyon baya ga 'Yancin kan Tibet', amma yaya 'Tibet mai 'yancin kai' ya ke? Babu wanda ya san wannan. Bayan haka kuma, ba mu gani hali mai kyau ba ta lamarin da ya faru a jihar Tibet ba, Sinawa da yawa sun ji rauni ko rasa rayukansu a sakamakon lamarin, amma bai jawo hankula ko kadan ba daga wadanda ke goyon bayan 'Yancin kan Tibet' na duniya ba gaira ba dalili. Bugu da kari kuma, bayan da na ga labarin da hanya ta talibijin CCTV 4 ta bayar, dangane da 'yan tawaye sun kone mata biyar, na yi mamaki sosai. A kasarmu, mutanen da suka fahimci wannan halin, wato jama'ar jihar Tibet sun samu ikon aiwatar da harkokin kanta, ba su da yawa. A cikin shirin musamman da Gidan rediyon kasar Sin ya shirya a internet, an hada da abubuwan da ke da nasaba da 'Makon al'adu na jihar Tibet na shekarar 2006', ta yadda ake iya sake tunani da wadancan kyawawan abubuwa. Na yi imani cewa, kasar Sin, da kuma jama'ar da ke zama a jihar Tibet, za su fasa burin 'yan ware na balle Tibet daga kasar Sin. A waje daya kuma, ina fatan gwamnatin kasar Sin za ta sarrafa halin da ake ciki a wurin, kuma Sinawa ba za su nuna damuwa kan rayuwarsu ba kamar yadda suka yi a da. Kazalika kuma, ina fatan kafofin watsa labaru na kasarmu suna iya daidaita nufinsu na bayar da labarai. Abin da ya fi sanya mini faduwar gaba shi ne, kullum kafofin watsa labaru suna bayar da labarai ba na gaskiya ba cikin sauri, amma su kan amince da kalaman karya da suka yi a hankali a hankali. Bayan haka kuma, na yi fushi sosai kan wadancan ayyukan da aka yi na hana wasannin Olympic na birnin Beijing ta lamarin nan."
Joaquin, mai sauraronmu daga birnin Barcelona na kasar Spain, ya rubuto e-mail cewa, "A wakilci aikin bude hanyar jiragen kasa ta Qinghai-Tibet, muna iya ganin babban cigaba da jihar Tibet ta samu wajen bunkasuwar tattalin arziki ta jihar, da zaman rayuwar jama'a na wurin, a sakamakon manufofin nuna fifiko da gwamnatin kasar Sin ta fitar, da kuma goyon baya daga jama'ar dukkan kasar. Daidai haka, ko shakka babu, nufin balle Tibet daga kasar Sin, ba zai samu goyon baya daga jama'a ba.
Wani mai sauraronmu na Italiya Giordano ya zirgi tashe-tashen hankula da aka tada a birnin Lhasa sosai ta waya da fax, ya bayyana cewa, ya nuna goyon baya sosai ga ayyukan da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen daidaita wannan batu.
Mr. Yu wani Basine dake a Faransa ya nuna adawa sosai ga laifin tada tarzoma a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa, ya nuna cewa, ya yi bakin ciki sosai don ganin mutuwar farar hula da yawa a batun. Mr. Yu ya ce, zaman al'ummar jihar Tibet ya samu kyatattuwa sosai a karkashin jagorancin gwamnatin kasar Sin a cikin shekaru da dama, wasu 'yan tawaye suna fatan saka siyasa cikin wasannin Olympic na Beijing ta hanyar yin amfani da batun neman 'yanci kan jihar Tibet, ko shakka babu, ba za su iya cimma burinsu ba. Ya amince da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta daidaita batun da kyau.
Mai sauraronmu na kasar Czech Jindrich Tomisek dake son harshen duniya sosai ya nuna a cikin Email dinsa cewa, "na ji bakin ciki sosai yayin da na sami labari game da tarzomar da wasu tsirarrun mutane suka tada a birnin Lhasa. Ina fatan mummunan batun ba zai kawo cikas ga ayyukan mika wutar wasannin Olympic na Beijing ba. Ina fatan za a gudanar da ayyukan share fage cikin lumana da kuma za a cimma nasarar yin wasannin Olympic na Beijing."
Mai sauraronmu na kasar Monaco Helene ta ce, abin kurkure ne da aka hada tashe-tashen hankula na jihar Tibet da wasannin Olympic na Beijing. Wasannin Olympic gasar karfi da kyan gani ce, amma ba filin nuna ayyukan siyasa ba, shi ya sa, wasu kafofin watsa labaru sun yi kuskure wajen hada tashe-tashen hankulan jihar Tibet da wasannin Olympic na Beijing. Tana fatan gasar wasannin Olympic na Beijing za ta cimma nasara sosai.
1 2 3 4 5 6 7
|