Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a birnin Ma'anshan
2020-08-19 20:12:07        cri
Yau Laraba da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki birnin Ma'anshan na lardin Anhui. Ya fara ziyarar aikinsa a birnin daga yankin kiyaye muhallin halittu na Xuejiawa, domin ganewa idonsa yanayin da kogin Yangtse ke ciki, da yadda ake kiyaye da farfado da muhallin halittu da sauransu.

Yankin kiyaye muhallin halittu na Xuejiawa yana gabashin kogin Yangtse, fadin yankin ya kai kimanin muraba'in mita dubu 657, a baya ya yi fama da babbar matsalar gurbatar muhalli. A shekarar 2019, birnin Ma'anshan ya fara aikin gyara yankin gabashin kogin Yangtse, inda ya fi mai da hankali wajen gyara muhallin yankin Xuejiawa. Ya zuwa yanzu, yankin Xuejiawa ya kasance abin koyi a fannin kiyaye muhallin halittu a birnin Ma'anshan.

Bayan ziyarar da ya kai yankin Xuejiawa, Xi Jinping ya kuma ziyarci sassan masana'antar kamfanin mulmula karafa na Baowu Magang, domin ganewa idonsa yadda kamfanin ke dawo da ayyukansa da kuma yadda yake gudanar da ayyukansa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China