Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya yi kira ga matasa da su bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban kasar
2020-08-17 20:41:24        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, kamata ya yi a ilimantar da matasan kasar, ta yadda za su bayar da sabbi da kuma gagarumar gudummawa ga ci gaban kasar.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kwamitin sojan kasar, ya bayyana haka ne, cikin wasikar taya murna da ya aikawa taron gamayyar kungiyoyin matasan kasar da gamayyar kungiyoyin daliban kasar, wanda aka bude a safiyar Litinin din nan a birnin Beijing,

Xi ya bukaci kwamitocin jam'iyyar da gwamnatoci a dukkan matakai, da su inganta shugabanci a aikin matasa, su kuma ci gaba da taimakawa gamayyar kungiyoyin matasa da ta dalibai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China