Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aika gaisuwa ga ma'aikatan lafiyar kasar
2020-08-18 20:57:23        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa ma'aikatan lafiya dake sassa daban-daban na kasar gaisuwa, gabanin ranar ma'aikatan lafiya na kasar. Yana mai cewa, ma'aikatan lafiya su ne kashin bayan ciyar da tsarin kiwon lafiya gaba.

Shugaba Xi ya ce, tun lokacin da aka samu barkewar cutar numfashi ta COVID-19, ma'aikatan lafiya da dama ba su bata lokaci ba, inda suka kasance a kan gaba ba dare ba rana wajen yakar wannan annoba.

Xi ya ce, ma'aikatan lafiya sun bayar da muhimmiyar gudummawa wajen yaki da wannan annoba, sun kuma nuna akidar ba da muhimmanci wajen kare rayuka ta hanyar sadaukar da kai da nuna kauna.

A don haka, Xi ya yi kira ga ma'aikatan lafiyar, da su ci gaba da nacewa kan mayar da jama'a a gaban komai, da martaba ka'idojin aikin lafiya, da kokarin neman kwarewar aiki, da ba da sabbin gudummawa wajen ciyar da matakan kiwon lafiyar kasar Sin gaba, gami da inganta lafiya da jin dadin jama'a.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China