Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci daukar karin matakai na bunkasa ayyukan kare aukuwar balai
2020-08-19 11:44:17        cri

Da yammacin jiya Talata 18 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ke ziyarar aiki a lardin Anhui, ya gana da al'ummun da ke filayen noma, a kauyen Xidanpo na gundumar Funan, dake birnin Fuyang na lardin Anhui.

Tsaye cikin garjin rana, shugana Xi ya bayyana cewa, "Ina matukar damuwa game da halin da al'ummar mu ke ciki a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, amma a duk lokacin da na ga wadannan mazauna yankunan karkara na samu madogara, da karfin gwiwar ci gaba da ayyuka da rayuwa, na kan ji sauki a rai na."

Shugaban na Sin ya kara da cewa, ya yi farin cikin ganin yadda tituna suke a share bisa tsari. Ya ce "Mu Sinawa mutane ne da muka sha fama da yakar bala'u tsawon shakaru dubbai, kuma har yanzu muna ci gaba da wannan yaki".

Ya ce wannan yaki bai sabawa yanayin rayuwa na ainihi ba. Hasali ma hanya ce ta cimma daidaito tsakanin mutane da sauran halittun abokan zama. Don haka yayin da ake bin wannan tsari, ya dace a ci gaba da kyautata matakan kariya daga aukuwar bala'u. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China