Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya ziyarci lardin Anhui
2020-08-19 11:19:10        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya fara ziyarar aiki a lardin Anhui dake tsakiyar kasar Sin, tun daga jiya Talata 18 ga watan nan. Yayin ziyarar ya isa kogin Huaihe, wanda bisa taswirar kasar shi ne ya raba arewaci da kudancin Sin.

Tun da fari dai, shugaban na Sin ya ziyarci ganuwar ruwa ta Wangjiaba, inda ya ganewa idanun sa halin da kogin Huaihe ke ciki, da kuma matakan kandagarkin ambaliyar ruwa, da ayyukan jin kai da ake aiwatarwa a wurin, tun bayan da aka fara fuskantar bala'in ambaliya a farkon shekarar nan.

Shugaba Xi Jinping, ya sha ba da umarnin daukar muhimman matakai, game da kare rayukan al'umma a matsayin babban burin gwamnati, tare da tsara manufofin kariya da shawo kan ambaliya, da aiwatar da ayyukan jin kai, tare da yin duk mai yiwuwa, wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Kaza lika shugaban na Sin, ya ziyarci kamfanin hada jakukkuna na Hongliang dake garin Wangjiaba, don ganewa idanun sa yanayin da ake ciki, na farfado da ayyuka bayan shan fama da cutar numfashi ta COVID-19.

Da yake a bana kasar Sin ke kammala wa'adin da ta tsara, na gina al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni, da kuma shirin ta na yaki da talauci, shugaban na Sin ya kai ziyarar musamman ga cibiyoyin samar da tallafi a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, yana mai jaddada kudurin gwamnatinsa, na tsame daukacin al'ummun kasar daga kangin talauci.

A zangon karshe na wannan ziyarar aiki, shugaba Xi jinping ya ziyarci wurin Xitianpo Zhuang Tai na kauyen Limin dake garin Cao Ji. Ya kuma ziyarci filayen noma, domin kara fahimtar halin da gonaki ke ciki.

Game da halin da ake ciki na yaki da annoba kuwa, shugaba Xi ya ce har yanzu da sauran rina a kaba, don haka ba za a yi kasa a gwiwa ba, wajen daukar matakai. Kaza lika Sin za ta ci gaba da himma da kwazo, wajen gano dabarun shawo kan tasirin ambaliyar ruwa, da kuma samar da agajin jin kai ga mabukata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China