Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata kasashen Asiya da Turai su kiyaye dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, in ji Wang Yi
2019-12-17 10:14:11        cri
Jiya Litinin, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a yayin taron ministocin harkokin wajen Asiya da Turai karo na 14 da aka yi a birnin Madrid, fadar mulkin kasar Spain, cewa, ya kamata mu aiwatar da manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, domin cimma burin kiyaye zaman lafiya da inganta bunkasuwar kasa da kasa. Manufar ita ce, muhimmiyar hanyar da za ta taimaka wajen warware kalubaloli daban daban dake gabanmu. Kana, burin duk wani tsarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, shi ne kiyaye zaman lafiya da neman bunkasuwar kasa da kasa. A don haka, ya kamata kasashen Asiya da kasashen Turai su zama abin koyi ga sauran kasashen duniya wajen aiwatar da wannan aiki, da kuma kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, tare da kiyaye tsarin cinikayyar kasa da kasa karkashin jagorancin kungiyar cinikayya ta duniya, wato WTO.

Wang Yi ya ce, akwai bukatar a yiwa kungiyar WTO kwaskwarima, kana bangarori daban daban su taimakawa WTO wajen dawo da kotun daukaka kara ta kungiyar.

Bugu da kari, a shekarar 2020, kasar Sin za ta gudanar da taron kasashen da suka kulla "yarjejeniyar kiyaye halittu iri daban daban" karo na 15, kasar Sin tana sa ran cimma sakamako mai gamsarwa, ta yadda za ta ba da muhimmiyar gudummawa ga kasashen duniya wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China