Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: yarjejeniyar tsakanin Sin da Amurka zai amfanawa duk duniya
2019-12-15 16:10:04        cri
Mamban majalisar gudanawa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da Miro Cerar, mataimakin firaminista, kana ministan harkokin wajen kasar Slovenia a Ljubljana. Sun kuma gana da manema labaru bayan ganawarsu, inda Wang Yi ya amsa tambayoyin da manema labarai suka yi masa game da yarjejeniya ta matakin farko da Sin da Amurka suka cimma kan tattalin arziki da ciniki, cewar Sin ba ta yarda da warware takaddamar ciniki ta hanyar kara buga haraji ba, saboda ba wanda zai cimma nasara cikin takaddamar. Sin ba ta amince da matakin matsin lamba na kashin kai ba, wanda ya sabawa ka'idojin kungiyar WTO. Sin da Amurka sun kai ga matsaya daya kan takardun yarjejeniya a mataki na farko tsakaninsu bayan sulhuntawa tsakaninsu, Amurka ta yi alkawarin soke harajin da take bugawa kayayyaki kirar kasar Sin bisa mataki-mataki. Yarjejeniyar dake da zummar cimma muradun kasashen biyu, wadda ta kasance sakamkon shawarwari kuma matakin dake bayyana mutunta juna da suke yi. Ya kara da cewa, yarjejeniya ta dace da bukatun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri kuma ta biya muradun jama'ar kasashen biyu kuma ta biya bukatun kasashen duniya baki daya, mataki ne da ya taimakawa kasashen biyu da su maido da dangantakarsu da samun bunkasuwa yadda ya kamata. Kazalika, ya karawa duniya kwarin gwiwa wajen samun bunkasuwar tattalin arziki wanda ke fuskanta koma baya, da ba da tabbaci ga zaman doka da oda ga tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China