Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya jaddada da manufar Sin game da tsaro a gabas ta tsakiya
2019-11-27 17:32:52        cri
A yau Laraba ne ministan harkokin wajen Sin wang Yi, ya gana da wakilan wasu kasashe dake halartar taro game da tsaro a gabas ta tsakiya, wanda ke gudana a nan birnin Beijing.

Cikin jawabinsa yayin ganawar, Wang Yi ya ce cimma nasarar wanzar da tsaro a gabas ta tsakiya, muhimmin batu ne da ya shafi daukacin kasashen dake shiyyar, da ma sassan kasa da kasa.

Ya ce cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a bikin bude taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa karo na 8 da ya gabata, shugaban na Sin ya gabatar da matsayar Sin, mai kunshe da shawarar watsi da manufar kebewar wasu sassan a fannin aiwatar da manufofin tsaro a gabas ta tsakiya, da gina managarcin tsarin tsaro ga kowa, da ci gaba da gudanar da hadin gwiwa mai dorewa tsakanin kasashen yankin

Game da hakan, wakilai mahalarta taron na birnin Beijing, sun jinjinawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa a fannin wanzar da tsaro da zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Wakilan sun kuma nuna matukar damuwa kan manufofin Amurka, game da yankin Falasdinu, da Syria da sauran kasashen gabas ta tsakiya. A ganinsu, zaman lafiya da daidaito a gabas ta tsakiya na iya yin tasiri ga wanzuwar su a ragowar sassan duniya, wanda hakan ke shaida bukatar inganta tsare tsare, da tallafawa daga dukkanin kasashen duniya, wajen tattauna manyan manufofin magance kara tabarbarewar yanayin tsaro a yankin na gabas ta tsakiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China