Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin na kokarin bude kofarta ga ketare
2019-12-06 11:09:20        cri

Jiya Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da abokan kasar Sin daga bangarori daban-daban a Seoul, baban birnin Koriya ta kudu, inda ya nuna cewa, Sin na kokarin kara bude kofarta ga ketare. Ba ma kawai Sin ta cika alkwarinta lokacin da ta shiga WTO ba, har ma ta rage matsaikacin harajin kwastanta zuwa kashi 7.5 cikin dari, adadin da ya yi kasa da na sauran kasashe masu tasowa da kuma wadanda kasuwarsu ke saurin bunkasa. Matakin da ya sa halin da Sin ke ciki na aiwatar da ciniki da kasuwanci ya daga zuwa matsayi na 31 daga 78 a shekarun biyu da suka gabata. Ban da wannan kuma, Sin ta sassauta sharadunan shiga cikin kasuwanninta, inda ta bude kofar masana'antun kera kayayyaki a duk fannoni, sai kuma sana'ar ba da hidima, ban da wannan kuma, Sin ta takaita jerin sana'o'i da ayyuka da aka haramta zuba jari a ciki zuwa 40. Wang ya kara da cewa, a ran 1 ga watan Jarairun badi, Sin za ta aiwatar da sabuwar dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, a kokarin samar da yanayin zuba jari mai kyau ga baki masu sha'awar zuba jari a cikin kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China