2019-12-16 21:32:23 cri |
Wang Yi ya bayyana hakan ne, a yayin taron ministocin waje na 14 na kungiyar ASEM, wanda ya gudana a birnin Madrid na Sifaniya. Yana mai cewa manufar cudanyar sassa daban daban, ba za ta yi nasara ba, har sai an wanzar da zaman lafiya, an kuma bunkasa ci gaba. Ya ce cudanyar sassa daban daban shi ne jigon warware kalubalen dake addabar duniya.
Ministan ya kara da cewa, ko wane irin tsari za a bi na cudanyar sassa daban daban, burin sa shi ne wanzar da zaman lafiya a duniya, da kuma samun ci gaba. Ya ce ya dace kasashen Asiya da na turai, su samar da wani misali a fannin kare cudayyar sassa daban daban, su nacewa manufar gudanar da al'amura a mataki na kasa da kasa da hadin gwiwar MDD a matsayin ginshiki, su kuma wanzar da tsarin ciniki da zai hade sassa mabanbanta, karkashin kungiyar cinikayya ta duniya WTO a martsayin ginshiki. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China