Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin ta raya kanta tare da taka rawa wajen bunkasuwar duniya baki daya
2019-12-06 11:21:29        cri

Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da wakilan bangarori daban-daban na kasar Koriya ta kudu jiya Alhamis, inda ya nuna cewa, gudummawar da Sin take bayar ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya a ko wace shekara ta haura kashi 30 cikin dari, matakin da ya sa Sin ta zama wani inji dake ingzia bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Har ila yau, Sin ta kubutar da mutane miliyan 850 daga kangin talauci, gudummawar da take bayarwa a wannan fanni ga duniya ya wuce kashi 70 cikin dari, wannan abin mamaki ne da ba a taba gani ba a ci gaban Bil Adama.

Wang Yi ya nuna cewa, ba kowa ne ke son ganin bunkasuwar kasar Sin ba, wasu suna yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti, da illata bunkasuwar ta, inda suke kira da a kowa cikas ga bunkasuwar kasar Sin. Saboda bambancin ra'ayoyi, da matakin nuna fin karfi, duk wadannan matakai ba za su yi nasara ba ko kadan. Ko wace kasa na da 'yancin bunkasa kanta, kuma wajibi ne a yi adalci da ko wace al'umma. Tunanin cacar baka bai dace da halin da muke ciki ba, kuma ba wanda zai yarda da manufar babakere. Babu wanda zai iya hana farfadowar al'umamr Sinawa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China