Matsalar samun kiba sosai a kewayen hanta ya kan zama gyambon hanta da ciwon hanta. Kwanan baya, masu nazari daga jami'ar Tsukuba ta kasar Japan sun gano cewa, idan masu kiba sun dauki mintoci fiye da 250 a ko wane mako suna yin tafiya cikin sauri, duk da cewa ba su iya rage kiba, kibar da ke taruwa a kewayen hantarsu za ta ragu, ta yadda hakan zai zage matsalarsu ta samun kiba sosai a kewayen hanta.
Masu nazarin sun yi bincike kan masu fama da matsalar kiba sosai a kewayen hanta su 169, wadanda shekarunsu suka wuce 30 amma ba su kai 69 a duniya ba. Wadannan mutane sun gamu da wannan matsala ce sakamakon cin abinci fiye da kima, da kuma rashin isasshen motsa jiki, a maimakon shan giya.
Masu nazarin sun raba wadannan mutane 169 zuwa rukunoni guda 3, wato A, B da C, bisa tsawon lokacin da suke shafewa suna tafiya cikin sauri a ko wane mako. Mutanen da ke cikin rukuni na A sun dauki mintoci 150 a ko wane mako suna yin tafiya cikin sauri, yayin da wadanda ke cikin rukuni na B suka dauki mintoci 150 zuwa 250 a ko wane mako suna yin tafiya cikin sauri, kana a cikin rukuni na C, sun dauki mintoci fiye da 250 a ko wane mako suna yin tafiya cikin sauri. Masu nazarin sun yi fatan ganin, ko ciwon da wadannan mutane suke fama da shi sakamakon samun kiba sosai a kewayen hanta ya ragu ko a'a bayan motsa jiki na tsawon watanni 3.
Sakamakon nazarin ya nuna cewa, idan tsawon lokaci da aka dauka wajen motsa jiki yana karuwa, to, kibar da ke taruwa a tsakanin kayayyakin cikin dan Adam suna raguwa, musamman ma ga wadanda su kan dauki mintoci fiye da 250 a ko wane mako suna motsa jiki.
Amma duk da haka, masu nazarin na Japan ba su tono alakar da ke tsakanin raguwar kibar da ke taruwa a kewayen hanta da kuma raguwar nauyin jiki ba, lamarin da ya nuna mana cewa, duk da cewa, motsa jiki yadda ya kamata kamar daukar mintoci fiye da 250 a ko wane mako wajen yin tafiya cikin sauri ba ya iya rage nauyin jikin dan Adam, amma yana iya rage kibar da ke taruwa a kewayen hanta, da kuma taimakawa samun daidaito a jikin dan Adam.
Nazarin da masu nazarin na Japan suka gudanar ya tunatar da mu cewa, lallai ya kamata a motsa jiki ba tare da kasala ba, ko da kuwa nauyin jikin mutum bai zai ragu ba. (Tasallah Yuan)