in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayanan masana game da fa'idar cin abinci a kimiyance ko bisa yadda jama'a ke tunani (B)
2019-11-28 17:22:49 cri

Akwai wasu kyawawan fasahohi da aka gada daga zuriya zuwa zuriya dangane da cin abinci. Masana kan abubuwa masu gina jiki suna ganin cewa, wasu ra'ayoyin da aka dade ana dogara a kansu da ake amfani da su. Ko mun amince da wadannan rashin fahimta ko a'a? Masu nazari daga kasar Amurka sun yi nazari kan wasu bayanai da aka baza dangane da amfanin abinci don tabbatar da gaskiyar wadannan bayanai ko kalamai.

Shin da gaske ne cakulan da matasa ke ci, shi ke sa kananan kuraje su fito a fuskarsu? A'a, ba haka ba ne! Kullum iyaye kan gaya wa 'ya'yansu matasa kada su ci cakulan da yawa, in ba haka ba, kananan kuraje za su fito a fuskarsu. Amma nazarin ya nuna mana cewa, babu wata alaka a tsakanin cin cakulan da kuma kananan kuraje dake fita a fuskar matasa. Kananan kuraje na fita a fuskar matasa ne sakamakon yawan maiko a jikin fatarsu, sa'an nan kuma, abubuwa masu kazanta, kwayoyin cuta da kuma matattun kwayoyin halitta su kan taru a cikin fatar, a karshe sai su taru su haifar da matsalolin fata ga matasa.

Masu nazarin sun ce, abun bakin ciki shi ne ba a san ainihin dalilin da ya sa kananan kuraje ke fita a fuska ba tukuna. Amma watakila sauyawar yawan sinadarin hormone a jikin dan Adam ta kan sanya maiko ya yi yawa a fuska. Duk da haka cin cakulan ba wani dalili ba ne, haka lamarin yake wajen cin pizza, soyayyen dankalin turawa siriri, da burodin da aka kunshe nama a cikinsa ko hamburger da cuku.

Amma masu nazarin sun yi nuni da cewa, a gaskiya sun gano wata alaka a tsakanin wani nau'in abinci da kuma kananan kuraje dake fitowa a fuska. Kayayyakin madara kan tsananta matsalar fata da matasa suke fuskanta, saboda watakila akwai sinadarin hormone cikin harawar da sa masu samar da madara suke ci. Don haka masu nazarin sun tunatar da wadanda ke da kananan kurji a fuskarsu da su tabbatar da cin kayayyakin madara masu inganci.

Yawancin matasa ba su mai da hankali kan lafiyar fatarsu sosai ba, su kan ce, mu matasa ne. Amma kamata ya yi a kiyaye lafiyar fatar jiki daga lokacin kuruciya. Fatar jiki na kokarin kare mutane daga kwayoyin cuta iri daban daban. Idan ta ji rauni, za ta bushe, ta zama ja, ta rika yin kaikayi, da dai sauransu, kana kuma za ta tsufa cikin sauri. Yaya muke kiyaye fatarmu yadda ya kamata? Kada a rufe fuska da wani abu don kyautata fata ba ta hanyar da ta dace ba. Kada a wanke fuska fiye da kima. Kada a wanke fuska da ruwa mai zafi. Kada a cire matacciyar fatar fuska kullum. Tilas ne a rika kare fatar fuska da ma duk fatar jiki daga hasken rana. Kada a yi amfani da kayayyakin kwalliya da abubuwan kyautata fata ba ta hanyar da ta dace ba. Idan kuma an gamu da matsalar fatar jiki, sai a je ga kwararren likita cikin lokaci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China