Akwai wasu kyawawan fasahohi da aka gada daga zuriya zuwa zuriya dangane da cin abinci. Masana kan abubuwa masu gina jiki suna ganin cewa, wasu ra'ayoyin da aka dade ana dogara a kansu da ake amfani da su. Ko mun amince da wadannan rashin fahimta ko a'a? Masu nazari daga kasar Amurka sun yi nazari kan wasu bayanai da aka baza dangane da amfanin abinci don tabbatar da gaskiyar wadannan bayanai ko kalamai.
Shin da gaske ne cin naman kifi yana kara basira ko a'a? E, haka ne. Ka yarda da maganar mahaifiyarka, musamman ma kananan yara! Yana da kyau kananan yara su ci naman kifi a kalla sau daya a ko wane mako, hakan zai tamaka musu yin barci mai kyau, tare da kyautata basirarsu. Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi kananan yara su rika cin naman kifi tun suna kanana.
Kowa ya san cewa, kifi yana da dauke da sinadarin Omega-3, kuma yana kara karfin basira da kyautata yin barci mai kyau. Amma mene ne alakar cin kifi, kara karfin basira da yin barci mai kyau? Don sanin amsar wadannan tambayoyi, Masu nazarin sun gayyaci kananan yara 541 wadanda shekarunsu suka wuce 9 amma ba su kai 11 da haihuwa ba, kuma yawan maza ya kai kaso 54, yayin da yawan 'yan mata ya kai kaso 46.
Sun tambayi wadannan kananan yaran adadin kifin da suka ci a watan da ya gabata, sun kuma jarraba basirarsu ta yin magana da sauran fannoni. Ban da haka kuma, iyayensu sun cika takardar tambaya dangane da tsawon lokacin barci da wadannan kananan yara suka dauka, ko su kan tashi da tsakar dare, ko suna son yin barci da rana da dai makamantansu.
Bayan da masu nazarin suka tantance bayanan da suka samu, sun gano cewa, basirar kananan yara da su kan ci kifi a ko wane mako ta fi ta wadanda ba safai ko kuma ba su cin kifi a ko wane mako ba yawa. Kana kara cin naman kifi yana taimakawa wajen kyautata ingancin barci.
Duk da haka, ba a ce, idan ka ci kifi a yau kashegari za ka samu maki mai kyau a jarrabawa ko kuma za ka yi barci mai kyau ba. Sakamakon da ake fatan samu, zai dauki tsawon lokaci ainun. Idan aka fara cin naman kifi mai cike da sinadarin Omega-3 da wuri, akwai yiwuwar hakan zai iya kara fahimtar mutum. Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, idan jarirai sun kai watanni 10 da haihuwa, ana iya ba su naman kifi.
To, wane irin nau'in kifi ne yake kunshe da sinadarin na Omega-3? Wadannan sun hada da nau'in kifin salmon, albacore tuna, mackerel, herring, sardine da dai sauransu. Haka zalika, hanya mafi dace wajen dafa wadannan kifaye ita ce gasawa, a maimakon soya naman kifi bayan da aka shafe naman da burodi. (Tasallah Yuan)