in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan masu ciki sun sha maganin kau da kwayoyin cuta, za su kara wa 'ya'yansu barazanar kamuwa da ciwo
2019-09-02 09:22:18 cri


Masu nazari daga kasashen Australiya da Denmark sun gano a kwanan baya cewa, idan masu ciki sun sha maganin kau da kwayoyin cuta, 'ya'yansu na iya kara fuskatar barazanar kamuwa da cututtuka sakamakon yadda kananan kwayoyin halitta dake jikinsu yayin da suke girma, kana kuma wadanda aka haife su kalau ba ta tare da yin tiyata ba sun fi saukin kamuwa da cututtuka sakamakon irin wadannan kananan kwayoyin halittu.

Cibiyar nazarin kananan yara ta Murdoch dake Australiya ta kaddamar da rahoton nazarinta a kwanan baya cewa, masu nazari daga cibiyar da takwarorinsu na jami'ar Aarhus ta Denmark sun tantance wasu bayanai da suka shafi kananan yara 'yan kasar Denmark dubu 770 wadanda aka haife su daga shekarar 1995 zuwa 2009, kana an kai su asibiti sakamakon yadda kananan kwayoyin halitta suka shiga jikinsu, da kuma yadda mahaifansu mata suka sha maganin kau da kwayoyin cuta yayin da suke dauke da ciki.

Masu nazarin sun gano cewa, idan masu ciki sun sha maganin kau da kwayoyin cuta, 'ya'yansu na iya fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka da kaso 20 sakamakon kananan kwayoyin halittan dake jikinsu bayan da aka haife su har zuwa lokacin da suka kai shekaru 14 a duniya, musamman ma kafin su haihu a lokacin da aka yi hasashe ko kuma sun tsawaita lokacin shan maganin a lokacin da suka samu ciki. Ban da haka kuma, idan masu juna biyu sun sha maganin kau da kwayoyin cuta, 'ya'yan da suka haifa ba tare da wata tangarda ba, sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka, gwargwadon wadanda aka haife su ta hanyar yin tiyata, a lokacin da suke girma.

Masu nazarin suna ganin cewa, wannan yana da nasaba da kananan kwayoyin halitta da ke cikin hanji. Jariran da aka haifa ba tare da wata matsala ba, kwayoyin halittu na shiga cikin hanjinsu ne daga hanjin mahaifansu mata da yadda aka haife su, yayin da jariran da aka haife su ta hanyar yin tiyata irin wadannan kananan kwayoyin halitta suna shiga cikin hanjinsu ne ta fatar mahaifansu mata da yanayin asibitin da aka haife su.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, shan maganin kau da kwayoyin cuta yana iya haifar da rashin daidaiton kananan kwayoyin halittu a cikin hanjin kananan yara. Kasancewar daidaiton kananan kwayoyin halitta a hanjin kananan yara yana da matukar muhimmanci ga matakan kariyar jiki da yin rigakafin kamuwa da cututtuka. Masu juna biyu kan kamu da ciwo sakamakon kananan kwayoyin halitta, don haka suna bukatar samun jinya yadda ya kamata, amma ya zama tilas a mai da hankali kan shan maganin kau da kwayoyin cuta ta hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China