in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan nauyin maza ya wuce misali a lokacin balaga, sai za su kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari
2019-07-22 15:45:29 cri

Kwanakin baya, masu nazari na kasar Sweden sun kaddamar da sakamakon nazari dake cewa, idan nauyin maza ya wuce misali a lokacin balaga, to za su fuskanci karin barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau'in 2 a nan gaba.

Masu nazari daga jami'ar Gothenburg ta kasar Sweden sun tattara bayanan mizanin BMI na awon nauyin jikin mutum da suka shafi maza dubu 36 a lokacin yarantarsu da kuma lokacin balagarsu, sun kuma sake bibiya kan lafiyarsu bayan da shekarunsu suka wuce 30 da haihuwa. Matsakaicin tsawon lokaci da masu nazarin suka dauka suna sake bibiya ya kai shekaru 30. Sun gano cewa, wasu dubu 1 da dari 7 da 77 sun kamu da ciwon sukari mai nau'in 2.

Masu nazarin sun kaddamar da sakamakon nazarinsu cikin mujallar "ilmin Endocrinology da yanayin sarrafa sinadaran jiki" ta kasar Amurka, inda suka nuna cewa, idan nauyin jikin wani saurayi ya wuce misali a lokacin yaranta, amma ya samu daidaiton nauyin jiki a lokacin balaga, barazanar da yake fuskanta wajen kamuwa da ciwon sukari mai nau'in 2 ba za ta karu ba. Amma idan nauyin jikinsa ya wuce misali a lokacin yaranta da kuma lokacin balaga duka, to barazanar za ta karu sosai. Alal misali, gwargwadon maza wadanda suka samu daidaiton nauyin jiki a ko da yaushe, barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau'in 2 kafin shekarunsu suka kai 55 a duniya da maza wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali a lokacin balaga suke fuskanta ta ninka sau 4 ko fiye da haka.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, ko da yake nazarinsu bai iya tabbatar da kasancewar wata alaka a tsakanin mizanin BMI din na maza a lokacin balaga da kuma barazanar kamuwa da ciwon sukari ba, sakamakon nazarin ya tunatar da iyaye da su mai da hankali kan nauyin jikin 'ya'yansu, su yi kokarin taimaka musu rage barazanar kamuwa da ciwon sukaru mai nau'in 2 bayan da suka yi girma.

An ba da shawarar cewa, kamata ya yi kananan yara su ci abinci ta hanyar da ta dace, su kara cin kayayyakin lambu, a maimakon kiba maras kyau, su kuma motsa jikinsu kullum. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China