in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ciwon sukari mai nau'in 2 yana da nasaba da raguwar tsawon rai
2019-07-22 15:43:19 cri

Kwanan baya, jami'ar Edinburgh ta kaddamar da wani sakamakon nazari da cewa, nazarin da suka gudanar kan 'yan kasar Scotland fiye da miliyan 3 ya nuna cewa, tsawon ran masu fama da ciwon sukari mai nau'in 2 bai kai tsawon ran wadanda ba su kamu da wannan ciwo ba. Amma masu nazarin sun nuna cewa, yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana taimakawa wajen kara hana tsanantar ciwon, da raunana illar da ciwon ke kawo wa lafiyar masu fama da shi.

A kasar ta Scotland, wani ko wata daga cikin wasu mutane 20 ne ke fama da ciwon sukari, a ciki kuma had da kaso 90 da suke fama da ciwon sukari mai nau'in 2, wanda aka kamu da shi saboda rashin aikin sinadarin Insulin da ke jikin mutum yadda ya kamata.

Kungiyoyin nazari karkashin shugabancin jami'ar Edinburgh ta tantance da kwatanta bayanan lafiyar 'yan kasar Scotland masu fama da ciwon sukari mai nau'in 2 fiye da dubu 250 wadanda ba a san sunayensu ba, da kuma mutane miliyan 2 da dubu 800 wadanda ba su kamu da ciwon ba. Shekarun wadannan mutane sun wuce 40 amma ba su kai 89 a duniya ba. Masu nazarin sun raba su cikin rukunoni daban daban bisa shekarunsu don yin bincike kan bambancin tsawon ransu, la'akari da matsayinsu ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa.

Sakamakon tantancewar ya nuna cewa, a cikin wadannan mutane, kome jinsi dinsu, shekarunsu da matsayinsu ta fuskar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar, tsawon ran masu fama da ciwon sukari mai nau'in 2 bai kai na wadanda ba su kamu da ciwon ba. Amma ba a gano irin wannan abu a cikin maza wadanda shekarunsu suka wuce 80 da haihuwa, kuma sun fi fama da talauci.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, bambancin tsawon rai ya sha bamban bisa mabambantan shekarun mutane. Alal misali, a cikin mata wadanda shekarunsu suka wuce 40 amma ba su kai 45 a duniya ba, tsawon ran wadanda ba su kamu da ciwon sukari mai nau'in 2 ba, ya fi na masu fama da ciwon yawa, har da shekaru 5 da rabi.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarinsu ya shaida cewa, idan ana neman tsawaita matsakaicin tsawon ran al'umma, ya zama wajibi a inganta yin rigakafi da shawo kan ciwon sukari mai nau'in 2 a cikin dukkan al'ummar kasa, kana kuma yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana taimakawa wajen yaki da ciwon sukari na nau'in 2. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China