in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barazanar zubewar ciki tana da nasaba da shekarun mata da haihuwa da kuma tarihin samun ciki
2019-06-11 13:47:16 cri


Jami'ar Bristol ta kasar Birtaniya ta bayyana rahoton nazarinta a kwanan baya cewa, barazanar zubewar ciki da mata suke fuskanta, tana da nasaba da shekarunsu da haihuwa, cututtukan da suka kamu da su sakamakon samun ciki, ciki had da zubewar ciki. Amma akwai bukatar zurfafa nazari kan dalilan da ke haddasa haka.

Kungiyar nazari ta kasa da kasa karkashin shugabancin jami'ar Bristol ta tantance bayanan da suka shafi yadda mata 'yan kasar Norway fiye da dubu 420 suka samu ciki daga shekarar 2009 zuwa 2013. Kungiyar nazarin ta yi bayani da cewa, ta zabi mata 'yan kasar Norway domin yin bincike ne saboda kasar ta Norway tana daya daga cikin kasashe kalilan da suke adana cikakkun bayana game da zubewar ciki a kowa ne lokaci.

Rahoton nazarin ya shaida mana cewa, mata wadanda shekarunsu suka wuce 25 amma ba su kai 30 da haihuwa ba sun fuskanci barazanar zubewar ciki mafi kankanta. Barazanar tana karuwa sosai bayan da shekarunsu suka wuce 30. Mata wadanda shekarunsu suka zarce 45 a duniya kuma barazanar da suke fuskanta wajen zubewar ciki ta kan kai kashi 53 cikin dari.

Sa'an nan kuma masu nazarin sun gano cewa, bayan da mata suka rasa cikin da suke dauke da shi sau daya, barazanar zubewar ciki da suke fuskanta ta kan karu da kashi 50 cikin dari. Kana kuma idan kuma cikin nasu ya zube har sau biyu, to. barazanar ta kan ninka sau biyu. Ban da haka kuma, idan mata sun kamu da ciwon sukari da sauran cututtuka sakamakon dake da alaka da samun ciki a lokacin samun ciki a baya, barazanar zubewar ciki idan sun sake samun ciki za ta karu.

Amma duk da haka, masu nazarin sun ce, sun gudanar da nazarinsu ne ta hanyar sa ido, rubuta bayanai, tantance su da kwatanta su. Kana kuma ba su kai ga yanke hukunci na karshe ba tukuna.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, nazarinsu ya shaida cewa, shekarun mata da haihuwa da kuma cututtukan da suka kamu da su sakamakon samun ciki suna kara barazanar zubewar ciki. Watakila zurfafa nazari kan irin wannan alaka, zai taimaka wajen gano dalilan da suke hadasa kamuwa da cututtukan da ake gamuwa da su sakamakon samun ciki da kuma zubewar ciki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China