in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu sun zama ayagi ne saboda kwayoyin halitta na gado
2019-06-24 10:10:29 cri

Mene ne dalilin da ya sa wasu su zama ayagi, su ke saurin fada da mutane cikin sauki? Ikon Allah ne ko kuma sun zama haka sakamakon muhallin da suke rayuwa? Masu nazari daga jami'ar Montreal ta kasar Canada sun yi nazari kan tagwaye 555. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, yawancin fadace-fadacen da kananan yara suka yi kafin shekarunsu su cika 6 da haihuwa suna da nasaba da kwayoyin halittu na gado, yayin da fadace fadacen da suka yi bayan shekarunsu sun cika 6 amma ba su kai 13 a duniya ba, ke da nasaba da muhallin da suke rayuwa.

Masu nazarin sun tantance tagwaye masu tsananin kama da juna 223 da kuma tagwayen da suka sha bamban da juna 332. Malaman wadannan kananan yara sun jarraba da kuma rubuta abubuwan da suka yi yayin da shekarunsu suka kai 6, 7, 9, da 10 a duniya, don kwatanta fadace-fadace iri 2 da wadannan tagwaye suka yi, wato yin wani abu ko yin magana don fin karfi ta yadda za su samu iko, da kuma mayar da martani kan barazanar da aka yi hasashen za a kai musu.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, muhimmin dalilin da ya sa kananan yara kai hari kafin shekarunsu su cika 6 da haihuwa shi ne domin kwayoyin halittu na gado. Yawancin kananan yara su kan rage fadace-fadace yayin da suke girma. Muhallin da suke rayuwa ya kan ba da tasiri ko kawo illa ga aikace-aikacen da kananan yara suka yi yayin da shekarunsu suka wuce 6 amma ba su kai 12 a duniya ba.

Masu nazarin suna ganin cewa, hakan ya nuna cewa, kananan yara suna girma yadda ya kamata, karfinsu na fahimta yana samun kyautatuwa, kamar tsara shiri, tsai da kuduri, sarrafa kansu da mai da hankali kan wani abu. Masu nazarin sun yi bayani da cewa, kada mu manta da wani abu, fada, wani muhimmin bangare ne na rayuwar kananan yara yayin da suke koyon al'adun zaman rayuwa, a kokarin dacewa da zaman al'umma. A lokacin da shekarun kananan yara suka wuce 2 amma ba su kai 5 a duniya ba, sun fi yawan yin fada a duk tsawon rayuwarsu. Amma su kan kyautata karfinsu na sarrafa kansu sannu a hankali yayin da suke girma a kwana a tashi, su kan daidaita rikici ta hanyar tuntubar saura. Kana kuma, su kan sanyaya zukatansu, don kaucewa kai wa saura hari.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, za su ci gaba da yin nazari kan wasu abubuwan musamman da suke da nasaba da yadda kananan yara suka ke fada. Har ila yau kuma wannan nazari ya jaddada muhimmancin ba da taimako ga iyalan da suke bukatar a taimaka musu da kuma ba da taimako ga wasu kananan yara a makarantu, lamarin da ya amfana wajen shawo kan wasu cututtukan tunani da kuma yin rigakafin kamuwa da su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China